dailytrust

Jan aikin da ke gaban Tinubu wajen haxa kan qasa

Daga Abiodun Alade, Legas da Sani Ibrahim Paki

Agata Litinin 29 ga watan Mayu, 2023 Asiwaju Bola Ahmed Tinbu zai zama sabin angon Najeriya bayan an rantsar da shi a matsayin sabon Shugaban Qasa. Zai sha rantsuwar ce bayan ya lashe babban zaven da aka gudanar ranar 25 ga Fabrairu - zaven da aka kwashe tsawon shekaru ba a samu irinsa ba, inda wanda ya yi nasara ya lashe shi da kaso mafi qaranci, tun bayan zaven 1979.

To sai dai masana harkokin siyasa da masu sharhi kan al’amuran yau da kullum na cewa, zaven ya zo ne a lokacin da qasar ke fama da qalubalen haxin-kan qasa ta vangaren addini da qabilanci da kuma vangaranci.

‘Tun bayan Yaqin Basasa, Najeriya ba ta tava shiga irin wannan yanayin ba’

A cewar tsohon Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN) kuma Sarkin Kano na 14, Malam Muhammadu Sanusi II, rabon da Najeriya ta fuskanci irin wannan rarrabuwar kan tun zamanin Yaqin Basasan da aka yi a shekarun 1969 zuwa1970.

Sanusi II, wanda ya bayyana haka yayin jawabinsa a wani Taron Qasa Kan Tattalin Arziki da Shugabanci don murnar cikar babban malamin addinin Kirista, Ituah Ighodalo shekara 62 a duniya, ya ce, sakamakon zaven da ya gabata, yanzu qasar ta dare gida biyu saboda bambancebambancen addini da na qabilanci.

Ya ce, “Yanzu wannan matsalar ta jefa shakku a zukatan jama’a a kan duk wata doka ko mataki da gwamnati za ta xauka bayan zave.

“Wannan ne ma ya sa a watan Oktoban bara, a yayin Taron Zuba Jari na Jihar Kaduna, na shawarci ’yan Najeriya cewa duk wanda ya ce musu magance matsalolin Najeriya a 2023 abu ne mai sauqi, kada su

zave shi, saboda bai san girman matsalar ba.

“Ba na tunanin qasar nan ta tava shiga halin tsaka-mai-wuya irin wannan tun bayan Yaqin Basasa. Muna fuskantar qalubalen sake gina qasa. Bambancebambancen addini da na qabilanci sun yi mana katutu, ga tattalin arzikinmu yana cikin tsaka-mai-wuya, sannan ga rarraunan shugabanci,” in ji Sanusi.

Sai dai masu sharhi kan al’amuran yau da kullum da shugabannin al’umma da sauran jagororin jam’iyyu suna ganin duk da wannan qalubale na rarrabuwar kan ’yan kasa ta fuskar addini da qabilanci, sabon Shugaban Qasar zai iya xinke duk wata varaka idan ya xauke su a matsayin tsintsiya maxaurinki xaya.

A cewar Shugaban Jami’ar Tarayya da ke Kashere a Jihar Gombe, Farfesa Umar Pate, akwai dalilai na ciki da waje waxanda suka haddasa matsalolin, amma alhakin sake haxe kan qasa na wuyan sabon Shugaban Qasar.

Sai dai shehun malamin ya ce, duk da cewar kantafin da aka yi da amanar al’umma ce musabbabin matsalolin da qasar ke ciki, waxanda suka haddasa kashe-kashe da lalata dukiyoyi da ma yunqurin vallewa daga qasa, akwai jan aiki wajen tabbatar da ci gaba da kasancewar Najeriya qasa xaya.

Ya ce, “Idan ka kalli Kundin Tsarin Mulkinmu da tsarin siyasarmu, duka za ka ga an tsara su ne ta yadda za su ba kowa damar da zai ji ana damawa da shi.

“Shawarata ga gwamnati mai zuwa ita ce ta kalli Najeriya a matsayin qasa xaya. Ta duba wasu tsare-tsaren da aka bi a baya (na haxa kan qasa) har aka zo inda ake yanzu.

“Magana ce ta tafiya da kowa ba tare da nuna bambanci ba, ta samar da dimokuraxiyyar da za ta sa kowa ya ga dalilin ci gaba da zamansa a qasar, ba yin abin da da gangan zai yi wa tsarin zaman tare zagon qasa ba,” in ji malamin.

Kalaman qiyayya da qin jinin juna

Shi ma wani fitaccen masanin harkar tsaro da leqen asiri, Dokta Kabiru Adamu, ya ce zargin nuna bambanci da wasu al’ummomi da wasu yankunan qasar nan ke yi wa gwamnati sun taka muhimmiyar rawa wajen sake rura wutar.

Kodayake ya ce sakamakon zaven 2023 ya nuna qarara yadda manyan ’yan takara suka yi amfani da bambancebambancen addini da qabilanci wajen cim ma buqatunsu na qashin-kai, yadda xan takarar PDP, Alhaji Atiku Abubakar da takwaransa na Jam’iyyar LP, Peter Obi suka koma kotun sauraren qararrakin zave don neman bahasi ya yayyafa wa wutar ruwa.

Ya ce, “Batutuwan da suka dabaibaye zaven 2023 da irin rawar da kusan dukkan manyan ’yan takara uku a zaven suka taka, da kuma yadda aka riqa yaxa kalaman qiyayya da na qin jinin juna a lokacin zaven, duk sun taka mummunar rawa a zaven da kuma sakamakonsa,” in ji shi.

Dangane da hanyar da ya kamata a bi wajen magance waxannan matsaloli, masanin, wanda shi ne Shugaban Kamfanin Beacon Consulting Limited, ya ce, “Ya kamata gwamnati mai jiran gado ta fito da nagartattun tsare-tsare da za su sake haxa kan qasa, su tabbatar da adalci da daidaito da janyo kowa a jika, ta yadda kowane vangare na qasar nan zai riqa jin ana tafiya tare da shi”.

Abin da ya wajaba a yi

Shi ma wani lauya masanin Tsarin Mulki, Kayode Ajulo ya ce, Tinubu na da jan aiki a gabansa wajen sake haxa kan qasar nan da magance matsalolin tsaro da samar da ayyukan more rayuwa da kuma bunqasa tattalin arziki.

Shi ma Farfesa Pate ya qara da cewa, baya ga magance waxannan matsaloli, ya zama wajibi sabuwar gwamnati ta magance matsalar cin-hanci da almundahana waxanda ya ce suna cikin manyan matsalolin da suke ci wa Najeriya tuwo a qwarya.

Ya ce, idan ’yan Najeriya suka fahimci yana da kyakkyawar aniya ta mutunta su ba tare da nuna bambanci ba, za su ba shi cikakken haxin-kai.

“Ina fata gwamnatin za ta mayar da hankali wajen magance rashawa da samar da ayyukan raya qasa da inganta ilimi da vangaren aikin gwamnati da adalci, kamar yadda dokokin qasa suka tanada wajen tsarin raba-daidai,” in ji Farfesa Pate.

Shi ma Dokta Kabiru Adamu ya shawarci sabuwar gwamnatin da kada ta yi wa tsarin shari’ar zaven da yanzu haka ake gudanarwa katsalandan, ta yadda za a ga kotunan a matsayin masu cin gashin kansu.

Rinjaye mafi qaranci

Shugaban Makarantar Development Specs Academy, Farfesa Okey Ikechukwu, shawartar dukkan masu ruwa-da-tsaki ya yi, musamman masu neman haqqoqinsu a kotu, da su mutunta kowane irin hukunci kotunan za su yanke a kan qararrakinsu na zave.

Ya ce, kodayake Tinubu ya lashe zaven ne da quri’u mafiya qanqanta tun bayan dawowar Najeriya mulkin dimokuraxiyya a 1999, hakan ba zai kawo masa wani tasgaro ba, tunda dai ya cika dukkan sharuxxan da doka ta tanada kafin lashe zave na samun quri’u mafiya rinjaye kuma a sassa daban-daban na qasar nan.

Sai dai ya ce akwai barazanar samun qaruwar rarrabuwar kai a fafutikar rabon muqamai, kamar yadda ake gani a wajen neman shugabancin Majalisar Dokoki ta Qasa.

“Rarrabuwar kan na daxa qaruwa yayin da ake ci gaba da kokawar neman muqamai, amma ina fata abubuwa za su inganta, da zarar Shugaban Qasa ya daidaita a kan mulki kuma ya rungumi kowa hannu bibbiyu.

“Ina kuma son Shugaban ya qyale ’yan Najeriya, musamman ’yan siyasa, su fahimci cewa ba mu da wata qasa da ta wuce Najeriya, ballantana mu yi tunanin lalata ta,” in ji shi.

Shugaban Jam’iyyar APC a Jihar Legas, Cornelius Ojelabi ya ce, yana da yaqinin babu makawa gwamnatin Tinubu za ta haxa kan ’yan Najeriya.

“Ba a kai ga rantsar da shi ba tukunna, amma idan aka yi la’akari da abubuwan da ya yi a baya, muna kyautata masa zaton zai qara haxa kai da kuma ciyar da qasar gaba. ’Yan Najeriya su qara haquri har a rantsar da shi tukunna, za su ga kyawawan manufofinsa sun fara aiki gadan-gadan,” in ji Shugaban na APC.

To sai dai masu magana da yawun PDP da wakilinmu ya buqaci jin ta-bakinsu sun qi su ce uffan, suna cewa ba abin da za su ce a kan gwamnatin har sai kotu ta yanke hukunci kan qarar da suka shigar suna qalubalantar zaven Tinubu.

Sakataren Yaxa Labarai na PDP na Qasa, Debo Ologunagba ya ce, har yanzu maganar sahihancin zaven Tinubu na gaban kotu.

Shi ma wanda ya gabace shi a kan kujerar, kuma Kakakin Kwamitin Yaqin Zaven Shugaban Qasa na Jam’iyyar a zaven 2023, Kola Ologbondiyan ya ce, “PDP tare da xan takararta na Shugaban Qasa Alhaji Atiku Abubakar, yanzu haka suna gaban kotu kan zaven. Don haka ba zan ce komai ba a kai har sai an yanke hukunci.”

Kazalika, xaya daga cikin masu magana da yawun kwamitin yaqin neman zaven na Atiku, Charles Aniagwu, wanda shi ne Kwamishinan Yaxa Labarai na Jihar Delta, ya ki cewa uffan a kai.

FRONT PAGE

ha-ng

2023-05-26T07:00:00.0000000Z

2023-05-26T07:00:00.0000000Z

https://dailytrust.pressreader.com/article/281513640524768

Media Trust Limited