dailytrust

Fulani sun yi asarar mutum 100 a rikicin Filato

— Miyetti Allah An kashe mutum 85- Muwaghagvul

Daga Hussaini Isah, Jos

Qungiyar Fulani Makiyaya ta Miyetti Allah ta Qasa, (MACBAN), reshen Jihar Filato ta ce Fulani sun yi asarar sama da mutum 100 a harin da aka kai a wasu qauyuka da ke Qaramar Hukumar Mangu, a makon jiya.

Qungiyar ta bayyana haka ne a wata sanarwa da ta fitar xauke da sanya hannun Shugaban Qungiyar, Malam Muhammad Nuru Abdullah.

Rundunar ’Yan sandan Jihar Filato, ta tabbatar da cewa mutum 87 ne suka rasa rayukansu a wannan hari.

A vangaren Qungiyar Qabilar Muwaghagvul ta yi iqirarin cewa ta rasa mutum 85 a harin da aka kai.

A sanarwar da Qungiyar Fulani makiyayan, ta ce sama da Fulani 200 da suka haxa da mata da qananan yara ne suka vata a wannan hari. Haka kuma, sama da mutum 100 sun rasa rayukansu.

Har ila yau, sanarwar ta ce, dabbobin Fulani da suka haxa da shanu da tumaki da awaki sun vata a yayin da aka kai waxannan hare-hare.

Ta ce, “Wannan wata mummunar munafa ce ta kisan qare-dangi da aka shirya wa al’ummar Fulani a qauyukan Bwoi da Kombun da Sarfal da Rinago da Jukga da Kuwes da Kaangag da Farin Qasa da Kerana da Lugga Dimeza da Fungong da Gindiri Gok da Bughan Gida da Millet da Rufwang da Tidiu da Dejwak Rufwang da Lupo da Wushik da sauransu. Zuwa yanzu an gano shanu 1,000 a hannun varayin da suka sace su, tare da taimakon jami’an tsaro.”

Sanarwar ta ce, a hareharen, maharan sun yi awon gaba ko kuma sun qona dubban dabbobi da kayayyakin al’ummar Fulani.

“Waxannan ayyyukan ta’addanci da aka yi wa al’ummar Fulani sun jefa su cikin mawuyacin hali da ya sanya dubbansu suka yi gudun hijira zuwa wasu yankuna na Qaramar Hukumar Mangu da sauran wuraren da suke maqwabtaka da qaramar hukumar,” in ji sanarwar.

BABBAN LABARI

ha-ng

2023-05-26T07:00:00.0000000Z

2023-05-26T07:00:00.0000000Z

https://dailytrust.pressreader.com/article/281539410328544

Media Trust Limited