dailytrust

An kashe varawon babur an qona gawarsa a Gombe

Daga Rabilu Abubakar, Gombe

Wasu fusatattun mutane a kusa da Babbar Kasuwar Gombe a maraicen Litinin sun kashe wani da ake zargin varawon babur ne kuma sun banka wa gawarsa wuta.

Ana zargin ya sace babur xin ne da wani ya shiga banki ya ajiye a gaban Bankin Ja’iz.

Wani ganau da ya nemi a sakaya sunansa ya ce, varawon ya nemi ya tsere da babur xin a lokacin da mai shi ya fito ya yi ihu varawo, inda nan take ’yan acava suka bi shi aka kama shi.

Ya ce, jama’a cikin fushi suka riqa dukansa suna buga masa dutse daga bisani suka kashe shi sannan suka cinna wa gawar wuta.

Ya ce, bayan an qona varawon ’yan sanda sun zo wajen sun tattara gawar suka tafi da ita.

“Mai babur xin da ya samu babur xinsa sai ya yi sauri ya bar wajen domin tsoron tambayoyin da zai iya fuskanta daga ’yan sanda a lokacin bincikensu,” in ji shi.

Da yake tabbatar da lamarin, Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Gombe ASP Mahid Mu’azu Abubakar, ya ce wanda ake zargi da satar tuni aka tafi da gawarsa zuwa asibiti don tabbatar da mutuwarsa.

Ya ce, duk da qona varawon da aka yi, likitoci ne kaxai za su iya tabbatar da mutuwarsa, inda ya ce sai lokacin da ya samu rahoton tabbacin ya mutu zai sanar da wakilinmu, wanda kuma har lokacin haxa wannan rahoton bai samu ba.

Sai ya yi kira ga jama’a su guji xaukar doka a hannunsu, inda ya ce hakan ba daidai ba ne.

BABBAN LABARI

ha-ng

2023-05-26T07:00:00.0000000Z

2023-05-26T07:00:00.0000000Z

https://dailytrust.pressreader.com/article/281543705295840

Media Trust Limited