dailytrust

An ci gaba da haqo mai a Borno

Daga Simon Echewofun Sunday da Sagir Kano Saleh

Kamfanin Mai na Qasa (NNPCL) ya ci gaba da aikin haqo xanyen mai a yankin Tafkin Chadi da ke Jihar Borno, bayan shekara shida da dakatar da aikin.

An ci gaba da aikin ne washegarin da Shugaban Qasa Muhammadu Buhari ya qaddamar da matatar mai ta Xangote, wadda ita ce mafi girma a Afirka da ake sa ran za ta taimaka wajen rage wahalar mai a Najeriya.

A shekarar 2017 ce aka dakatar da aikin neman mai a rijiyoyin mai masu suna Wadi-1 da Kinasar-1, da ke yankin Tuba, sakamakon harin da mayaqan Boko Haram suka kai wa ma’aikatan da ke aiki a lokacin.

Sai dai daga bisani, bayan bincike da samun tabbacin tsaro, NNPC ta ci gaba da aikin a shekarar 2022 a rijiyar mai ta Wadi-B.

Babban Daraktan NNPCL, mai kula da haqo mai, Mukhtar Zanna, ya ce kamfanin ke amfani da fasahar zamani, kuma yana da qwarin gwiwar samun xanyen mai da iskar gas da dangoginsu a rijiyar.

A nasa vangaren, Aminu Maitama, wanda shi ne Babban Daraktan Ayyukan Haqar Mai na NNPCL, ya ce, “Mun yi amanna cewa yawan xanyen man da za a samu a yankin zai isa kasuwanci.”

Aikin ya samo asali ne a 1976, da aka fara binciken gano xanyen mai, a yankunan Gubiyo da Maiduguri da kuma Baga, kafin a ci gaba da shi a 1996.

BABBAN LABARI

ha-ng

2023-05-26T07:00:00.0000000Z

2023-05-26T07:00:00.0000000Z

https://dailytrust.pressreader.com/article/281560885165024

Media Trust Limited