dailytrust

Gwamnan Gombe ya zama Shugaban Qungiyar Gwamnonin Arewa

Daga Sani Ibrahim Paki

Gwamnan Jihar Gombe, Alhaji Muhammadu Inuwa Yahaya, ya zama Shugaban Qungiyar Gwamnonin Arewa (NGF).

Hakan ya biyo bayan zaven da qungiyar ta gudanar a ranar Talatar da ta gabata.

Gwamna Inuwa wanda aka zava a wa’adin farko a matsayin Gwamnan Gombe a shekarar 2019, ya sake lashe zave a karo na biyu a zaven 2023 da aka kammala a watan Maris duk da qalubale da ya fuskanta.

Zai karvi ragamar shugabancin qungiyar ce daga Gwamnan Jihar Filato mai barin gado, Gwamna Simon Lalong, bayan ya shafe shekara huxu yana jagorancin ta.

Shi dai Gwamna Lalong ya kammala wa’adin mulkinsa na biyu, inda ya yi takarar sanata amma bai yi nasara ba.

Gwamna Lalong ne Darakta Janar na yaqin zaven zavavven Shugaban Qasa, Bola Tinubu a zaven da ya gabata.

A jawabinsa na godiya, Gwamna Inuwa ya yi alqawarin yin duk mai yiwuwa wajen sauke nauyin da aka xora masa ba tare da la’akari da bambancin jam’iyya ba.

“Za mu yi aiki tuquru domin tabbatar da mun ciyar da yankinmu gaba domin

yin kafaxa-da-kafaxa da qasashen duniya ta hanyar samar wa mutanenmu romon dimokuraxiyya,” in ji shi.

Ya ce, yankin Arewa na zaune a saman man fetur da iskar gas mai ximbin yawa da sauran albarkatun qasa, wanda a cewarsa qungiyar ba ta da wani uzurin rashin yin duk mai yiwuwa wajen haqowa domin cin gajiyar yankin baki xaya.

A vangaren Gwamna Lalong ya buqaci sabon shugaban qungiyar ya yi amfani da qwarewarsa wajen ciyar da qungiyar gaba.

Ya ce, a shekara huxu da ya

yi yana jagorancin qungiyar, Gwamnonin Arewa ya sha fama da matsaloli da dama, sannan ya yi kira ga sababbin gwamnonin yankin su yi aiki tare domin tabbatar da zaman lafiyar yankin.

“Mun sha fama da matsaloli da dama, amma da haxin kan gwamoni da taimakon Gwamnatin Tarayya da jami’an tsaro, mun samu nasara bakin gwagwado,” in ji shi.

Qungiyar Gwamnonin Arewa, qungiya ce ta dukkan gwamnonin Arewa ba tare da la’akari da bambancin jam’iyyarsu ba.

BABBAN LABARI

ha-ng

2023-05-26T07:00:00.0000000Z

2023-05-26T07:00:00.0000000Z

https://dailytrust.pressreader.com/article/281590949936096

Media Trust Limited