dailytrust

Dalilan gaza shawo kan matsalar wutar lantarki — Injiniya Usman Yusuf

Daga Adam Umar, Abuja

Yaya za ka bayyana fa’ida da rashin fa’idar sayar da vangaren wutar lantarki da a ka yi a baya? Ba wutar lantarki kaxai ba, duk wata harka irin ta kamfani ta fi inganta a qarqashin xan kasuwa a madadin gwamnati. Tafiyar da kamfani a qarqashin ’yan kasuwa shi duniya ta sa a gaba a yanzu saboda ya fi samun inganci a qarqashin wannan tsari. Shi xan kasuwa ya fi lura da sa ido a kan sana’a fiye da yadda gwamnati za ta kula da shi. Zai ci gaba da havaka shi yana faxaxa shi don ribarsa ta yawaita, da hakan zai samar da aikin yi da kuma bunqasa tattalin arzikin qasa. Sannan a gefe guda gwamnati za ta samu sukunin gudanar da sauran al’amura kamar na sa ido da zama alqali a kan yadda kamfanoni suke gudanar da aikinsu. Sai dai shi xan kasuwa riba ya sa a gaba ba zai kashe tarin kuxi don kai wuta inda ba zai samu riba sosai ba kamar yankunan karkara da ke da qarancin jama’a da kuma rashin masu buqatar wutar sosai. Wannan shi ya sa duk da cewa gwamnati ta sayar da kamfanonin, amma ta ci gaba da riqe wasu vangarorinsa don ci gaba da ganin ana damawa da ita, sannan tana tallafawa wajen kai wuta zuwa yankunan karkara a qarqashin wata hukumarta mai suna Rural Electrification Agency (REA) da sauransu. Harkar cefanar da kamfanoni musamman irin na wutar lantarki ba a sayar wa kamfani sai an tabbatar yana da abokan hulxa qwararru musamman a vangarori biyu, wato technical partners

da commercial partners. Technical partners su ne qwararrun abokan hulxa wajen sannin makamar aiki, sannan Commercial partners waxanda ke da kuxin da ake buqata don inganta harkar da sanin yadda za a gudanar da shi har ya xore ta hanyar samun riba. Wannnan ina jin yana xaya daga cikin abubuwan da aka gaza kula da su a lokacin sayar da kamfanonin, sai aka sa son kai da ke jawo matsalar.

Kamfanonin samar da wuta na zargin waxanda ke da alhakin rarraba shi da qin sayen wutar da suka samar, yaya batun yake?

Da gaske ne akan samu hakan inda kamfanonin da ke samar da wutar za su samar da shi, amma sai su masu alhakin rarraba shi ga jama’a wato Discos, su qi xaukar wutar saboda rashin kuxin saya. Har ta kai ga kamfanonin da ke samar da wutar na tunanin sayar da shi kaitsaye ga masu sayar da shi wanda kuma a gaskiya za a samu matsala a doka. Xaya daga cikin matsalar da ke jawo haka ita ce gazawa ko rashin qwarewar kamfanonin sayar da wutar. Ba su san yadda za su karvi kuxin ba, sun gaza samar da adadin mita na zamani da ake buqata, ya kamata su xauki tsarin kamfanonin sadarwa. Sun fuskanci matsaloli masu yawa har ta kai kuxin da suka ranta daga bankuna suka sayi kamfanonin daga hannun gwamnati, sun gaza biya, wa’adin da aka yanka masu ya wuce. Sai ragamar kamfanonin ya koma qarqashin bankunan da suka samar da kuxin. Sai dai qwace kamfanonin da bankuna suka yi ba abu ne mai kyau ba saboda ba

Injiniya Usman Yusuf qwararre ne a harkar wutar lantarki inda ya yi aiki da rusasshen Kamfanin Sadarwa na Qasa (NITEL) da Hukumar Samar da Wutar Lantarki a Karkara a baya-bayan nan. Ya kuma yi aiki a kwamitoci ciki har da na Minista Babatunde Fashola lokacin da ya riqe Ma’aikatar Wuta. A yanzu yana zaman kansa tare da cigaba da ba da gudunmawa a harkar. Ya zanta da Aminiya kan matsalar wutar lantarki da yadda yake jin za a magance ta: abu ne mai yiwuwa, amma dole sai an sauya tunani da halin da ake bi a wajen tafiyar da lamarin, saboda wanda ake kai a yanzu ba zai tava inganta lamarin ba. Ana xaukar abin ne vangare-vangare, alhali shi kuma sha’anin wutar lantarki vangarori uku ne da shi da suke buqatar tafiya bai-xaya. Sha’anin wutar lantarki ya kasu kashi uku, akwai vangaren samar da wutar wato Generation, sai tura shi zuwa garuruwa wato Transmission da kuma aikin rarraba shi ga al’umma da kuma amsan kuxi wato Distribution. To idan ka ce vangare guda kaxai za ka fi fifitawa wajen zuba jari kamar na Generation da muka fi yi a baya, sai ka ga ba abin da aka yi. Dole ne a dubi lamarin gaba xaya, sannan a sauya tunanin da ake da shi a kai. Ma’ana ba yadda za a yi a samar da wutar lantarki har megawatts 10 kaxai ba, a’a yaya za yi al’umma su samu megawatts 10. Ka ga abu ne da ke buqatar samar da rukuni ukun nan a lokaci guda. Dole sai an xauki abin kwatankwacin murhun tukunya da ake yi a da wato duwatsu uku. Kuma sai mun sauya halayenmu tun a wajen ba da aikin kwangila. Misali akwai wani kwamiti na minista da na kasance a ciki a lokacin ma’aikatar na qarqashin Fashola, ba a kai ga rarraba ta ba, sai ya kula cewa akwai tarin ayyukan IPP Project da dama ba a kammala ba suna warwatse a ko’ina kara- zube. Yawancin ayyukan kwangilolin an ba da su ne ba tare da tantancewa kan inda ayyukan za su bi su kai ga inda ake nufi ba, wato abin da ake kira safiyo. Misali daga garin Maqarfi zuwa Zariya akwai babban layin wuta da ya ratsa ta wajen da ya kamata a sake ga qaramin tashar wuta da aka yi irin wannan aikin a wajen. Amma bayan kammala aiki ba tare da tantance ta inda aikin wutar zai bi ya kai ga inda a ka yi aikin ba, sai aka gano cewa akwai matsala, a haka aka yi fatali da aikin har aka zo ana lalata dukiyar da aka zuba a wajen. A yanzu haka akwai wuta mai qarfin megawatts 15 ta wajen ba ta yadda za a ci gajiyarta. Sai kamfanonin da ke gudanar da ayyukan wutar lantarki ne ke zuwa suna cire na’ura daga jikin wanda aka samar a wajen suna kaiwa ga ire-iren na’urorinsu a wuraren da aka fuskanci matsala. Ka ga an yi asarar aikin ke nan, waxanda aka yi abin dominsu ba su ci gajiyar ba. Dole sai an sauya yadda ake ba da ayyukan kwangiloli kara-zube ba tare da tantancewa ba. Akwai buqatar a samu manajojin tsare-tsare a vangarorin ba da ayyukan, waxanda za su riqa tsara su tare da yin hasashe ko ana buqatar aiki a wuri kafin a kai da kuma yiwuwar hanyar da za a bi wajen kai aikin, a maimakon yin alfarma ga wuraren da suke da uwa a gindin murhu kuma a daina ba da aikin ga waxanda ake son a azurta dare guda. Dole a riqa baje aikin a faifai, a zavi cancanta wajen kai aikin a wuri da kuma waxanda suka da ce su yi aikin.

Dole sai an sauya yadda ake ba da ayyukan kwangiloli kara-zube ba tare da tantancewa ba. Akwai buqatar a samu manajojin tsare-tsare a vangarorin ba da ayyukan, waxanda za su riqa tsara su tare da yin hasashe ko ana buqatar aiki a wuri kafin a kai da kuma yiwuwar hanyar da za a bi wajen kai aikin, a maimakon yin alfarma ga wuraren da suke da uwa a gindin murhu kuma a daina ba da aikin ga waxanda ake son a azurta dare guda. Dole a riqa baje aikin a faifai, a zavi cancanta wajen kai aikin a wuri da kuma waxanda suka da ce su yi aikin.

hurumin banki ba ne gudanar da harkar wutar lantarki. Yin haka koma-baya ne domin bankuna ba su da qwarewa a harkar gudanar da wutar lantarki ba za su kuma iya jure lamarin ba, na tabbata a qarshe dole za su nemi masana abin, don a samu mafita.

Me za ka ce kan kammala aikin tashar wutar lantarki ta Zangeru da ake shirin qaddamarwa da kuma takwaranta ta Mambila da ke neman gagarar kundila?

Kammala aikin tashar wutar Zangeru babban ci gaba ne da zai samar da qarin wuta megawatts 700 ga qasar nan. Sai dai ko rabin-rabin na Mambila bai kai ba da ke da qarfin iya samar da wuta megawatts

3050. An samu bambancin tun a farkon ba da aikin, shi na Mambila an sa son rai a ciki. Matsalar cin hanci ta sa an xauki wasu mutane an yi kwantaragi da su da ya zamewa qasar nan matsala.

A qarshe wace hanya kake jin za a bi don inganta wutar lantarki a qasar nan?

Inganta wutar lantarki a qasar nan

BABBAN LABARI

ha-ng

2023-05-26T07:00:00.0000000Z

2023-05-26T07:00:00.0000000Z

https://dailytrust.pressreader.com/article/281608129805280

Media Trust Limited