dailytrust

An samar da sunduqan adana kayan marmari na tsawon wata uku

Daga Aliyu Babanqarfi, Zariya

An samar wa ’yan kasuwar kayan marmari irin na lambu, musamman masu safarar tumatyr daga jihohin Arewa zuwa Kudu sunduqan adana kayansu har na tsawon wata uku domin rage musu asarar da suke tafkawa.

A yayin bikin buxe cibiyar sanyaya kayan lambu a wata qwarya-qwaryar biki da aka gudanar a harabar kasuwar Ɗan Magaji da ke Qaramar Hukumar Zariya, Jihar Kaduna, qungiyoyin masu noma kayan marmari da ’yan kasuwa da sarakunan yankin ne suka halarta.

Cibiyar adanawar wadda ke tattare da kayan zamani da za su riƙa sanyaya amfanin gona kamar tumatir da kabeji da albasa da sauransu da ake nomawa.

Kuma ana iya adana abubuwa kamar su kifi da nama da madara su kai kusan wata uku ba su lalace ba.

Kamfanin ColdHub da haɗin gwiwan Heifer International suka samar wa manoma da sunduqan da nufin rage asarar kayansu musamman tumatur da sauransu.

Da yake jawabi a wurin

?????????????? taron, babban jagoran Kamfanin ColdHub, Mista Nneameka Ikegwuonu ya ce tsarin na ColdHub an samar da shi a wasu jihohin Arewa da Kudancin Najeriya, kuma mutane na amfani da shi saboda yana taimakawa wajen adana abubuwan da ake nomawa a Najeriya tsawon lokacin ba tare da sun lalace ba.

A cewarsha manufar samar da tsarin a Zariya shi ne saboda gari ne da yake da ximbin manoma da suke noma kayan gwari, kuma ana samun koma -baya a lokuta da yawa saboda rashin samun kulawar da ta dace.

Ya gode wa al’ummar yankin saboda ba su haɗin kai da goyon baya a cikin shiryeshiryensu.

Da yake jawabi Mai martaba Sarkin Zazzau Malam Ahmed Nuhu Bamalli wanda Sarkin Yaƙin Zazzau Alhaji Yahaya Pate ya wakilta ya yaba wa qoqarin kamfanin na samar da cibiyarsa a Zariya inda manoma da dama za su amfana.

Wasu daga cikin manoman da suka halarci taron sun nuna farin cikisu da samar da wannan tsari, kuma suka yi fata tsarin zai ƙara taimaka wa kayan da suke nomawa lokutan rani da damina.

BABBAN LABARI

ha-ng

2023-05-26T07:00:00.0000000Z

2023-05-26T07:00:00.0000000Z

https://dailytrust.pressreader.com/article/281616719739872

Media Trust Limited