dailytrust

Ya tsinci Naira miliyan 18 ya ba mai shi, shi kuma ya ba shi tukicin Naira 1,000

Daga Adam Umar, Abuja

Wani matashi da ke sayar da lemon kwalba da ruwan roba a Abuja mai suna Aminu Usman, na ci gaba da shan albarka daga jama’a bayan ya mayar da Naira miliyan 18 da rabi da ya tsinta ga mai kuxin a Abuja.

Matashin wanda xan asalin qauyen Kola ne da ke qaramar Hukumar Birnin Kebbi a Jihar Kebbi, na gudanar da kasuwanci ne a Unguwar Zone 4 a kusa da cibiyar hada-hadar canjin kuxi ta Abuja.

A zantawarsa da Aminiya, Aminu wanda ya ce bai wuce kamar huxu da zuwa Birnin Tarayyar ba, bayan kammala makarantar sakandare a gida, ya fara kasuwanci ne don tallafa wa kansa da iyayensa.

Ya ce ranar da lamarin ya faru kamar mako uku a yanzu, ya xauko hajarsa ce zuwa bakin titi a kusa da inda yake zama, sai ya yi kicivis da baqar leda yashe a qasa.

“Na binciki cikin ledar sai na gane cewa kuxi ne a ciki, bayan na ci gaba da tafiya da nufin qarasawa inda nake zama sai na kula da mai kuxin yana tafiya yana ta dube-dube cikin damuwa. Nan take na kira shi tare da tambayarsa abin da yake nema, kuma ya yi mini bayani. “Sai na miqa masa kuxin ya yi mini godiya. Har na wuce sai ya kira ni ya ba ni tukuicin naira dubu xaya, ni ma na yi masa godiya na wuce,” in ji shi.

Aminu ya ce a yayin miqa kuxin, wasu da suka shaida lamarin sun buqaci mai kuxin ya tantance adadin kuxin, kuma a lokacin ne mai kuxin ya ambaci cewa kuxin a daidai suke Dala dubu 24, wato kimanin Naira miliyan 18 da rabi a farashin canji na Kasuwar Bayan Fage. Aminu ya ce daga baya bayan ya sanar da lamarin ga wasu maqwabtansa a wajen kasuwanci, sai aka buqaci mai kuxin wanda xan canji ne a unguwar, ya ware wani abu mai tsoka ya ba shi a matsayin tukuici, maimakon Naira dubu xaya da ya bayar.

Aminu ya ce zai yi amfani da tukuicin da ya samu wajen qarfafa kasuwancinsa na sayar da lemo da ruwan sanyi.

Alhaji Xanlami Jos shi ne Mataimakin Shugaban Masu

Aminu Usman

Harkar Canjin, ya ce bayan ya samu labarin ya buqaci ganin mai kuxin, inda ya yi masa qorafin cewa tukuicin Naira dubu xaya da ya bayar ya gaza. “Na shaida masa cewa kamata ya yi ya ba shi abin da ya xara haka don qarfafa gwiwa ga na baya kan sanar da tsintuwa irin haka idan ya faru. “Da farko ya yi kukan cewa kuxin ba nasa ba ne, amma bayan xan lokaci, sai ya ba shi Naira dubu 20.

Wani xan uwan matashin da ake kira Yaron Malam da ya fara yaxa lamarin a Intanet, ya ce wasu daga cikin waxanda suke bibiyarsa a dandalin sada zumunta sun taimaka da saqon abin alheri da ya miqa ga matashin.

BABBAN LABARI

ha-ng

2023-05-26T07:00:00.0000000Z

2023-05-26T07:00:00.0000000Z

https://dailytrust.pressreader.com/article/281625309674464

Media Trust Limited