dailytrust

An kama korarren xan sanda kan zargin fashi da makami

Daga Ahmed Mohammed, Bauchi

Rundunar ’Yan sandan Jihar Bauchi ta kama wani korarren xan sanda mai suna Muhammed Jawat mai shekara 27 da wasu mutum biyu, Muhammed Ahmed mai shekara 27 da Hussaini Ahmad mai shekara 19 bisa zargin aikata fashi da makami da riqe makami ba bisa qa’ida ba a jihar.

Kakakin Rundunar, Ahmed Mohammed Wakil ne ya bayyana haka a wata sanarwa da rundunar ta fitar a Bauchi.

Sanarwar ta qara da cewa: “Rundunar ’Yan sandan ta kai samame ne a ranar 25/4/2023 da misalin qarfe 4:36 na yamma inda ta kama mutum uku, Muhammed Ahmed mai shekara 27 daga Qofar Dumi, a birnin Bauchi da Hussaini Ahmad mai shekara 19 daga Qaramar Hukumar ItasGadau da kuma Muhammed Jawat mai shekara 27, korarren xan sanda (kurtu) daga qauyen Tulu a Qaramar Hukumar Toro.

“Lokacin da aka samu rahoto daga wani mutumin kirki a Qaramar Hukumar Jama’are, an tura jami’an ’yan sanda suka binciki motar da suke ciki, kuma aka kama waxanda ake zargi.

“A yayin bincike, an gano

qaramar bindigar guda xaya da harsasai biyu a hannunsu da suka gaza bayar da gamsasshen bayani kan yadda suka samu ko abin da za su yi da haramtacciyar bindigar.

“Waxanda ake zargin sun amsa laifin da ake zarginsu kuma suna taimaka wa ’yan sanda da bayanai masu amfani, bayan haka za a gurfanar da su a gaban kotu domin yanke musu hukunci,” in ji sanarwar.

Rundunar ’Yan sandan Jihar ta kuma kama wasu mutum 14 da ake zargi da aikata laifuffuka dabandaban da suka haxa da satar waya da fashi da makami da sata da kuma yunqurin fasa gidaje.

BABBAN LABARI

ha-ng

2023-05-26T07:00:00.0000000Z

2023-05-26T07:00:00.0000000Z

https://dailytrust.pressreader.com/article/281633899609056

Media Trust Limited