dailytrust

Matatar Xangote za ta magance matsalar kuxi ta alkinta wa Najeriya Dala biliyan 30 duk shekara - Emefiele

• Ya ce CBN ya samar da Naira biliyan 125 • Xangote ya yaba wa qarfin hali da tallafin Emefiele

Awani vangare na ci gaban tattalin arziki, Babban Bankin Najeriya a shekara da shekaru ya tallafa wa muhimman ayyuka don qarfafa tattalin arziki da kawo bunqasar qasa. Saboda muhimmancinta wajen bunqasa tattalin arziki, Matatar Xangote tana xaya daga cikin muhimman ayyukan da Bankin CBN ya zuba jari musamman wajen samar da rancen kuxi don tabbatar da aikin ya tabbata.

Hakan ya sa Gwamnan Bankin CBN, Godwin Emefiele ya bayyana cewa bankin ya tallafa wa Matatar Xangote da kuxi a cikin gida har Naira biliyan 125 da kuma Naira biliyan 75 a matsayin bashi ta hannun wasu zavavvun bankunan Najeriya.

Emefiele ya bayyana haka ne a ranar Litinin a wajen qaddamar da Matatar Xangote a Legas.

“A Satumban, 2013, lokacin da Alhaji Aliko Xangote ya sanar da shirinsa kan matatar, an qiyasta za ta ci Dala biliyan 9, inda Rukunin Kamfanonin Xangote zai zuba jarin Dala biliyan 3, yayin da sauran za a nemo bashi ne daga bankunan kasuwanci.

“Amma sakamakon wasu matsaloli an kammala matatar a kan Dala biliyan 18.5, inda aka raba samar da kuxin gida biyu Xangote ya zuba jarin rabi rabin kuma aka ciyo bashi. Ina farin cikin bayyana cewa rancen gudanar da matatar mafi yawa ya fito ne daga bankunanmu na cikin gida, saura kuma daga bankunan qasashen waje.

Babban Bankin Najeriya kamar kullum ya haxa hannu da Kamfanin Xangote wajen tabbatar da nasarar kammala matatar wajen samar da kimanin Naira biliyan 125 na kuxin a cikin gida da ake buqata don aikin,” in ji Emefiele

Emefiele ya qara da cewa, “Bankin CBN ta hanyar tallafin kuxaxen ayyukan ci-gaba, ya ci gaba da tallafa wa muhimman sassa na tattalin arzikin Najeriya don qarfafa masana’antun gida don daidai tattalin arzikinmu tare da qarfafa dogaro da kai.

“Ganin matatar za ta qarfafa yunqurinmu na faxaxa harkokin tattalin arziki ta hanyar fitar da tataccen man da ya saura, ya sa CBN ya tallafa wa aikin ta hanyar shirinmu na Samar da Kuxi da Inganta Kayayyakin Qanana da Matsakaitan Kamfanoni (SMERRF).

A qarqashin wannan shiri, kimanin Naira biliyan 75 aka ba aikin ta hanyar bankuna domin a qara qarfafa kamfanoni da samar da aikin yi da samar da kuxaxen musaya,” in ji shi.

Matatar za ta alkinta wa Najeriya kuxin musaya Dala biliyan 25

Har way au Gwamnan CBN xin ya ce Matatar Xangote za ta yi matuqar bunqasa

asusun ajiyar waje na Najeriya inda za ta alkinta wa Najeriya kuxin musaya Dala biliyan 25 sakamakon kawo qarshen shigo da fetur daga waje tare da samar da Dala biliyan 10 na makamashin da za a fitar.

Ya ce idan Najeriya ta gaza alkinta kuxaxen shigo da makamashinta, kuxin shigo da makamashin zai haura zuwa Dala miliyan 30.

Emefiele ya ce fara aikin matatar ya zo da ximbin alfanu, ta hanyar xaukar ma’aikatan dindindin dubu 135 da megawatt 12 na wutar lantarki, “yayin da matatar za ta ba mu damar qarin adana kuxaxe da rage nauyin kuxi.”

Ya qara da cewa, “Kashi 30 cikin 100 na kuxaxen musaya da ake buqata suna tafiya ne wajen shigo da mai, kuma yana da kyau a fahimci cewa a bisa bayanan kuxaxen ya qaru daga Dala biliyan 8.4 a shekarar 2017 zuwa Dala biliyan 23.3 a qarshen 2022.

“Aqalla kuxin shigo da fetur daga waje zai iya kaiwa Dala biliyan 30 nan da shekarar 2027, idan muka ci gaba da dogaro da shigowa da shi.Matatar za ta tserar da Dala biliyan 25 na kuxaxen musaya kuma ta samar da qarin Dala biliyan 10 ta hanyar fitar da fetur waje,” in ji shi.

Ya ce, daga shekarar 2017, kuxin matatar ya tashi daga Dala biliyan 9 zuwa Dala biliyan 18.5 inda Xangote ya zuwa rabin jarin. Ya ce, Rukunin Kamfanonin Xangote ya biya wasu daga cikin basussukan lafin qaddamarwar,

inda zuwa yanzu jimillar bashin da ya saura ya yi qasa daga Dala biliyan 4 zuwa Dala biliyan 2.7.

Ribar matatar

Ya qara da cewa, kammalawar ta buxe sabon shafi a fagen masana’antun Najeriya das hi kansa Kamfanin Xangote da Najeriya da kuma Nahiyar Afirka.

“A yau an sake rubuta tarihin Najeriya na qara gusawa gaba wajen bunqasa da ci gaba a vangaren kamfanonin harkar fetur.

“Cikakkiyar sadaukarwa don kammala matatar, duk da ximbin matsaloli na nuna misalin qoqarin da ake yi na gina qarin harkokin tattalin arziki.

“Wannan gini ya qunshi matata da kamfanin sinadarai da kamfanin takin yuriya da zai iya samar da tan miliyan uku na takin yuriya a shekara, kuma matatar za ta iya tace mai ganga dubu 650 a kullum, wadda ita ce mafi girman dunqulalliyar matata da ake da ita, kuma za ta iya samar da man da ake buqata a Najeriya har ta samar da kuxin musaya,” in ji Emefiele.

Shigar harkar fetur ta faro ne shekara 20 baya – Xangote

Da yake jawabi a wajen qaddamarwar, Xangote ya ce sha’awar shiga harkar fetur ta faro ne shekara 20 da suka gabata, inda ya ce niyyar ta haxu da ximbin matsaloli.

Sai dai ya nuna farin cikinsa kan yadda matatar ta tabbata. Ya qara da cewa Shugaba

Muhammadu Buhari ne ya qarfafa shi kan kada ya karaya wajen gina matatar.

Matatar Xangote ita ce dunqulalliyar matata guda xaya mafi girma a duniya kuma ita ce matata mafi girma a Afirka.

“Mai girma Shugaban Qasa da manyan baqi, tafiyar doguwa ce mai cike da qalubale. Ba za ta yiwu ba ba domin goyon baya da haxa hannu da vanagrori da dama da xaixaikun mutane.

“Don haka masu girma da manyan baqi ku ba ni dama in bayyana tare da godiya ga kaxan daga cikinsu.

“Bari in farad a Mai girma Shugaba Qasa. Ka ci gaba da tallafawa da qarfafawa a shekara takwas da suka gabata, a gare ni ka zama babban mai ginshiqi mai qarfafawa. A lokutan da na karaya qarfin gwiwarka da kalaman qarfafawa sun canja al’amura. Mai girma Shugaban Qasa ina miqa maka cikakkiyar godiyata,” in ji Xangote.

Xangote ya kuma gode wa gwamnatin Jihar Legas, inda ya faro daga zamanin zavavven Shugaban Qasa Bola Tinubu wanda ya mulki Legas daga 1999 zuwa 2007 har zuwa kan Gwamna mai ci Babajide Sanwo-Olu.

“Mutane irina da suka mayar da Legas gidanmu mun tabbatar tun daga dawowar wannan dimokuraxiyya, gwamnatin Jihar Legas ta fita daban wajen sadaukarwa da tallafa wa kamfanoni masu zaman kansu.

“Tun daga zamanin zavavven Shugaban Qasa Mai girma Asiwaju Bola Ahmed Tinubu wanda ya kafa cibiyar kasuwanci ta Lekki Free Zone, zuwa Gwamna mai ci Mai girma Babajide Sanwolu wanda ya fi tsayuwa don ganin an kammala wannan matata, gwamnatin jihar ta nuna cikakkiyar sadaukarwa wajen qarfafa samar da yanayi mai kyau wanda ya ba rukunin kamfanoninmu damar zuba jarin sama da Dala biliyan 30 a kamfanoni dabandaban a harkokin tattalin arzikin jihar a wannan lokaci.

“Ina cike da farin cikin miqa cikakkiyar godiya da jinjina ga Gwamnatin Jihar Legas da gwamnoninta kan sadaukarwarsu wajen samar da wannan kyakkyawan yanayi,” in ji shi.

Alhaji Xangote ya kuma yaba wa Gwamnan Bankin CBN, Mista Godwin Emefiele, wanda ya bayyana da “babban ginshiqin” tabbatar da nasarar matatar.

A jawabin Manajan Daraktan Kamfanin Mai na Qasa (NNPC), Malam Mele Kolo Kyari, ya ce qaddamar da matatar ta samar da wani muhimmin tsaro ga qasa.

A saqonninsu na fatar alheri shugabannin qasashen Ghana,Nana Akufo-Adoo da na Jamhuriyar Nijar, Mohammed Bazoum da na Senegal, Macky Sall da zavavven Mataimakin Shugaban Qasa, Kashim Shettima da kuma Gwamnan Jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, duka sun yi cikakken yabo kan samar da matatar.

BABBAN LABARI

ha-ng

2023-05-26T07:00:00.0000000Z

2023-05-26T07:00:00.0000000Z

https://dailytrust.pressreader.com/article/281668259347424

Media Trust Limited