dailytrust

Alaqa tsakanin qabila da halaye

Wai shin likita ana iya danganta xabi’a da qabila a kimiyyance? Misali kamar a danganta Fulani ko Barebari da wasu xabi’u? Daga IK Maiduguri Amsa:

Idan na fahimce ka ba al’adu ba ko xabi’u kake nufi, kamar son karatu da son kasuwanci da lalaci da sauransu ko? To haka ne ana iya danganta wasu qabilu da wasu xabi’u ko halaye, wasu masu kyau, wasu marasa kyau. Kowace qabila tana da halayenta na gari da halaye ko xabi’u marasa kyau. A kimiyyance za a iya alaqanta wannan da qananan qwayoyin halittu na DNA. Akwai ma wani fage na ilimin kimiyya na musamman a kan wannan wanda ake kira Ilimin Qananan Qwayoyin Halittu da Halaye wato wanda ya mai da hankali a kan dalilan da suka sa ake ganin wasu halaye da xabi’u a wasu qabilu, amma ba a ganin su a wasu da kuma yadda al’umma xaixaiku a qabila xaya sukan bambanta da juna.

Misali an san qabilar Hausawa da son kasuwanci, amma ba sa son yawo, su kuma qabilar Fulani an san su da son kiwo kuma ba sa son zama wuri xaya. A waje kuma, qasashen Larabawa an fi sanin su da son hutu ko hutawa, su kuma Turawa an fi sanin su da son neman suna. Haka nan Allah Ya yi kowa da nasa irin halayen. To ka ji.

Sauran tambayoyi

Ko yaya ake masu lanqwasa jiki suke kwalmaxa jiki ba sa jin ciwo ko karaya? Daga Aliyu Musa Kankiya Amsa: Masu lanqwasa su ma wasu bayin Allah ne da ke da bambancebambance na halitta da mu. Wato yawancinsu akwai wani abu da babu a gavovinsu da yake sakin gavar ta juya yadda suke so. Misali binciken hoto na masu lanqwasa ya nuna wasunsu da dama ba su da gurin-guntsi a wasu gavovi, abin da ake kira ligaments. Wasunsu kuma qashin ne ya tsage ya warke ya bar wurin yadda zai iya motsi. Wato wasunsu ba sa yin sana’ar tun asali sai daga baya da wani abu ya faru suka ga wurin yana motsuwa duk inda suka juya shi. Wasunsu kuma binciken hotuna sun tabbatar komai lafiya, amma suna yawan atisaye tun suna qanana har gavovin suka saki.

Me ya sa idan aka harbi wasu da bindiga a wuri yakan sa su rasa rai, wasu kuma sukan rayu? Daga Musbahu Xanjani Amsa:

Yawanci ya danganta da yawan jinin da aka zubar. Wani za a harbe shi a qirji, amma harsashin bai fasa ko naman wurin ba, wani kuma sai ya fasa naman wurin ya shiga ya fasa qashi, wani kuma ya fasa nama da qashi ya shiga ciki ya samu magudanar jini ya fasa, jini ya yi ta zuba a ciki ba a sani ba. To inda ake samun salwantar rai ke nan, yawan zubar jinin da ba a san da shi ba.

SIYASA

ha-ng

2023-03-24T07:00:00.0000000Z

2023-03-24T07:00:00.0000000Z

https://dailytrust.pressreader.com/article/281685439094007

Media Trust Limited