dailytrust

Masoyiyata kayan miyan sun burge ki?

WWani ne ya ga wata kyakkyawar budurwa a kasuwa ya ɗauki Naira 1000 ya rubuta lambar wayarsa a jiki, ya matsa kusa da ita ya ce, ’yan mata kin yar da kuɗinki. Ta sa hannu ta karɓa, ta kalli lambar ta ce, ta gode. Ta sayi kayan miya da Naira 1000 nan ba tare da ta ɗauki lambar wayar ba. Da dare ya yi, mai kayan miyar nan ya riƙa turo wa mutumin nan saƙon karta-kwana, yana cewa masoyiyata, rabin raina, abar ƙaunata, kayan miyan sun burge ki! A tunaninsa lambar ta budurwar ce.

WATA SABUWA

ha-ng

2023-05-26T07:00:00.0000000Z

2023-05-26T07:00:00.0000000Z

https://dailytrust.pressreader.com/article/281685439216608

Media Trust Limited