dailytrust

Mazan ko matan?

Daga Maryam Ali Kura

Mace: Da wahala ka samu wani namiji wanda ya san haqqin aure kafin ya mallaki mace, duk wanda ya ji mazantakarsa nan take za ka ji ya fara neman aure, ko da kuwa bai san haqqoqinsa ba.

Namiji: Au, to ai ba namiji ne kaxai yake da haqqoqi ba, mata nawa ne suka karanci auren kafin su yi? Sau da yawa mace takan zo gidan miji hannu rabbana ne, wai shi zai koyar da ita.

Mace: Me kake nufi? Da wane ne zai koyar masa da ita? Ai haqqinsa ne ya kuvutar da ita daga wuta, ya sanar da ita addininta.

Namiji: Wannan ai daban, shi ne zai koya mata tsabta, gyara kai, soyayya, iya riqe miji da daddare ko da rana, mallakar zuciya? Ko shi zai koya mata yauqi, iya zance, daxin murya da iya girki?

Mace: Da yake ku ba kwa laifi, sau nawa mace takan yi duk abin da za ta iya amma bai gani ba ya je yana xauko ’yar iska! Karuwar kan titi!

Namiji: Wannan duk rashin ilimin ne, kuma galibi shi yake vata aure, amma mace mai ilimi ai namiji a hannunta yake duk bala’insa.

Mace: Mnh! Ka faxa ka ji daxi, ai wallahi ba mai iya wa wannan halittar sai Mahaliccinta.

Namiji: Matakin farko ke nan na rusa gidanki, ai duk yadda wuta ta kai da quna ruwan sanyi kashe ta yake yi murus, don me Allah Ya kira matan Annabi da masu gida? Domin nasu ne, ke a yanzu in kika so mai gidanki ya zama kamar xan jariri a gabanki wallahi za ki iya, sai yadda kika yi da shi komai zafinsa.

Mace: Komai zafinsa fa ka ce! Namiji: Ai ko ya fi wuta quna. Mace: To gaya min.

Mace: Yauwa zo nan, me ka ce za ka gaya min?...Ka fin nan, jiya bayan mun rabu Nana Hauwa bint Muhammad ta tabbatar min da cewa, maza ba su da haquri, xan abu kaxan su fara shirin saki, ga su ba su kula duk adon da mace take yi musu.

Namiji: Ba ki karanta darussan Madabo ba ne game da aure?

Mace: Wane ne kuma Madabo? Namiji: Misbahu Saminu Madabo, ai malami ne babba, ya yi darussa da dama a kan matsalolin mace tsakaninta da mijinta.

Mace: Au ba namiji ba ne? Ai ba ta sake zani ba, kai dai faxi ra’ayinka kawai in na ji ya yi min in karva.

Namiji: Hahaha! To yanzu ba ki ganin mata su ke janyo hakan saboda rashin kula da kai a cikin gida? Galibi matar Malam Bahaushe ba ta ado sai za ta fita, kai hatta yara qanana sukan fahimci mamansu za ta unguwa in suka ga ta canja kaya.

Mace: Mhn! Namiji ke nan, to yaya kake so ta yi? Ita ce sharar gida da safe, kintsa yara su tafi makaranta, yi maka kayan karin kumallo, wanke-wanke, shirya xakinta, waxannan kafin ta gama su wasu yaran sun dawo, ga shirin abincin rana, shi ma kafin ta kammala ga na dare, a ’yan tsakani dole ta wanke tsummokaran yara, to kashi nawa kake so ta rabu? Ina wani lokacin ado? Kuma wasu kayan za ta sa ta yi aikin gida da su?

Namiji: Ai kin ji, to amma idan za ta fita waje za ta iya sanya kyawawa ko? Tana da lokacin ado da kwalliya, ke hatta lalle a yau matanmu in kin ga sun yi wallahi ba don mijin suka yi ba!

Mace: Ki ji har yana wallewa, to don wa za ta yi, mazan wasu?

Namiji: Ni dai ban ce ba.

Mace: Wallahi haka maganarka take nufi, ni wallahi ban tava yin lalle don wani qato ba, ina da mijina a gida, don Allah nake abina, kuma don shi.

Namiji: Sake dai Hajiya, galibin mata in kin ga sun yi lalle, to suna da wani sha’ani ko Qaramar Sallah ko Babba ko Mauludi da sauransu.

Mace: To yaya kake so ta yi? Sai ta ce masa wannan lallen don kai na yi ko me?

Namiji: A! Ba ki ji abin da A’isha (RA) ta ce ba lokacin da aka tambaye ta game da lalle? Ta ce: Launinsa yana ba Annabi (SAW) sha’awa, amma bai son warinsa, ba laifi ki yi tsakanin jini biyu ko yayin kowane jini. Amma ba batun biki ko sha’ani, in kin yi sai ki gaya masa, don shi kika yi don ya ji daxi, in sunansa Lawal ne sai ki rubuta (L) in kuma Xanlabaran ne sai ki rubuta (X).

DUNIYAR

ha-ng

2023-05-26T07:00:00.0000000Z

2023-05-26T07:00:00.0000000Z

https://dailytrust.pressreader.com/article/281719798954976

Media Trust Limited