dailytrust

An yanke wa ’yan fashi hukuncin kisa

Daga Abdurrahman Masagala, Benin

Wata kotu a Jihar Ekiti da ke Kudu ta yanke wa wasu mutum uku hukuncin rataya bisa samunsu da laifin satar waya da abin cajinta ta hanyar amfani da makami.

Mutanen su ne Omotayo Deji da Chidiebere Ifeanyi da kuma Bolaji Usman da sauran da ba a kai ga kama su ba, waxanda aka samu da laifin haxin baki da fashi da makami.

A cewar mai gabatar da qarar an kama mutanen ne a watan Mayun 2019 a Ava Elinfang, kan titin Federal Polytechnic d ake Ado Ekiti, an kuma gano wayoyi tarho da kwamfuta da takalmi da caja da abin cajin waya na Power Bank da sauran kayayyaki da kuxinsu ya kai Naira 186,000. Sannan an same su da wuqaqe da allunan katako a lokacin da suke fashin.

A ranar 21 ga Junairun 2020, aka gurfanar da waxanda ake zargin da fashi a gaban Mai shari’a Bamidele Omotoso, na Babbar Kotun Ekiti a Ado Ekiti.

A rahoton ’yan sanda da aka gabatar yayin shari’ar, xaya daga cikin waxanda abin ya shafa ya bayyana yadda waxanda ake qara suka kutsa cikin xakinsa da qarfe 7:30 na safe, suka yi masa barazana da bindiga suka tilasta masa bayar da dukiyarsa. Kuma sun lakaxa wa waxanda abin ya rutsa da su duka, inda suka samu raunuka a jikinsu, sannan suka tsere.

A yayin shari’ar, xan sanda mai gabatar da qara Kunle Sina Adeyemo ya gabatar da shaidu waxanda suka tabbatar da tuhumar da ake yi musu, ciki har da shaidar wanda aka kashe da wanda ake tuhuma.

Bayan sauraron lauyoyin waxanda ake qara, Mai shari’a Omotojo ya samu waxanda ake tuhuma da laifin fashi da makami, kuma ya ce masu gabatar da qara sun tabbatar da cewa waxanda ake tuhuma sun aikata laifin, inda ya yanke musu hukuncin kisa ta hanyar rataya.

DUNIYAR

ha-ng

2023-05-26T07:00:00.0000000Z

2023-05-26T07:00:00.0000000Z

https://dailytrust.pressreader.com/article/281775633529824

Media Trust Limited