dailytrust

NAPVID ta horar da naqasassu a Jihar Edo

Daga Abdurrahman Masagala Benin

Hukumar Kula da Naqasassu ta Jihar Edo (NAPVID) ta qaddamar da wani shiri mai taken Skill-Up a Benin, fadar jihar, domin horar da naqasassun sana’o’i daban-daban.

Da take jawabi a wajen bikin, Uwargidan Gwamnan Jihar, Betsy Obaseki, ta shawarci waxanda suka ci gajiyar shirin su yi iya qoqarinsu wajen aiki da abin da suka koya kuma kada su xauki naqasarsu a matsayin abar da za ta hana su samun nasara.

Betsy Obaseki, wacce Godsent Erhunmwunse ya wakilta, ta yaba wa Hukumar NAPVID kan vullo da shirin, inda ta ce mai naqasa shi ne mutumin da ba ya da wani abin da zai taimaka wa al’umma.

“Ya kamata ku sani cewa zamanin da muke ciki yanzu ba zamanin nuna takardar kammala karatu ba ne kaxai. Zamani ne na abin da za ku iya yi ta hanyar fasaha. Wato qwararrun mutane waxanda suke iya canza labarin duniya,” in ji ta.

Melody Omosah, Babban Daraktan NAPVID, ya ce shirin ya kasance ne don sanin cewa idan aka samar da yanayi mai dacewa, naqasassu na iya bayar da gudunmawa ga al’umma.

Omosah, ya yaba kan goyon baya da gwamnatin jihar ke ba shirye-shiryen NAPVID, ya ce taron ya kasance ci gban shirin Project Help ne da aka qaddamar a watan Mayun 2021, domin kula da lafiya, ilimi da kuma rayuwar naqasassu.

Shugabar Qungiyar Naqasassu ta Qasa (JONAPWD) reshen Jihar, Ann Ojugo, ta gode wa waxanda suka shirya taron.

DUNIYAR

ha-ng

2023-05-26T07:00:00.0000000Z

2023-05-26T07:00:00.0000000Z

https://dailytrust.pressreader.com/article/281779928497120

Media Trust Limited