dailytrust

Xangote ya bar tarihi

Ranar Litinin da ta gabata rana ce wacce a tarihin matatar mai mallakar fitaccen attajirin nan Alhaji Aliku Xangote take da matuqar muhimmanci.Domin a ranar ce ya amshi baqi daga ciki da wajen qasarmu da suka halarci buxe matatar da ya gina a yankin Lekki a Jihar Legas. Ko shakka babu dole a jinjina wa Xangote irin yadda aikin mai ke wahala musamman a wurare

kamar NNPC da su DPR. Dangane da rawar da gwamnati ta taka, dole ne a jinjina mata wajen ba Xangote goyon baya domin kawo qarshen zaman kashe wando a tsakanin matasa. Allah Ya ja zamanin mai rukunin kamfanonin Xangote. Wannan matatar mai Allah Ya albarkace ta, jama’a su amfana. Su kuma waxanda aka xauka aiki su zamo na qwarai masu amana da kwatanta gaskiya.

Saqo daga Mukhtar Ibrahim Saulawa Katsina. 07066434519 / 08080140820.

Taya Xangote murna

Alhaji Aliko Xangote ina taya ka murnar kammala gina matatar man fetur da ka yi a Legas, wadda aka yi bikin buxewa a ranar Litini. Allah Ya sa gina wannan matatar da ka yi ya kawo qarshen qarancin man fetur da muke fuskanta a wasu loqutan a Najeriya da ma Afirka baki xaya.

Saqo daga Abbakar Lawal Gidan Xanmaye Jargava. 09122667051

DUNIYAR

ha-ng

2023-05-26T07:00:00.0000000Z

2023-05-26T07:00:00.0000000Z

https://dailytrust.pressreader.com/article/281784223464416

Media Trust Limited