dailytrust

A ceto ilimi daga durqushewa a Zamfara

Na yi wannan matashiyar ce, kasancewar har yanzu xaliban da suka kammala rubuta jarrabawar NECO da WAEC na bara suna cike da burin ganin sun ci gaba da karatunsu domin amfanin kansu da al’umna, amma har yanzu wasu suna jiran tsammani.

Gwaggwavan kaso daga cikin waɗannan xalibai iyayensu talakawa ne masu rayuwar hannu-baka, hannuƙwarya, to ta yaya za su xauki nauyin karatun ’ya’yansu?

A shekarun baya kaɗan, a makarantun gwamnati, har kayan makaranta ake ɗinka wa ɗalibai domin ƙara masu ƙwarin gwiwar yin karatu. A ɓangare ɗaya kuwa iyayen yara suke cike da farin ciki saboda suna ganin an ɗauke masu wani nauyi, kuma suna kallon ’ya’yansu suna ci gaba da samun ilimi ba tare da wata matsala ba.

Babban abin takaici ne matuƙa, yadda aka yi wa ɓangaren ilimi riƙon sakainar kashi a Jihar Zamfara, idan aka yi la’akari da halin rashin tsaron da jihar ke fuskanta.

A bisa haka muna roko haɗi da kira ga sabuwar gwamnatin zaɓaɓɓen Gwamnan Jihar, Alhaji Dauda Lawal Dare idan an rantsar da shi a kan ya kafa wani kwamiti na musamman wanda zai binciki masu ruwa-da-tsaki, waɗanda alhakin wannan fanni ya rataya a wuyansu, kuma suka yi wa ɓangaren kallon bahagon kare don magance matsalar.

Daga Nura Muhammad Mai Apple Gusau, Shugaban Ƙungiyar Matasa ’Yan Gwagwarmaya ta Ƙasa. 08133376020

DUNIYAR

ha-ng

2023-05-26T07:00:00.0000000Z

2023-05-26T07:00:00.0000000Z

https://dailytrust.pressreader.com/article/281788518431712

Media Trust Limited