dailytrust

Yadda ake Miyar Marghi Special

Daga Elizabeth Fidelis

Barkanmu da sake haxuwa a wannan shafi namu na girkegirke, inda a yau za mu kawo wa uwargida yadda ake yin miyar Marghi Special.

Kayan haxi

Kifi tarwaxa Yakuwa Alayyaho Albasa Tattasai Attarugu Kanumfari Gyaxar qamshi Tumatir Sinadarin xanxano Man gyaxa Kanwa ko ruwan toka

Yadda ake haxin

· Da farko uwargida za ki gyara yakuwa sai ki yayyanka daidai yadda kike so, ki wanke da gishiri ta fita tas sai ki ajiya a gefe.

· Sannan ki gyara alayyaho ki yayyanka yadda kike so sai ki wanke da gishiri ya fita tas ki ajiya a gefe.

· Wanke kifi tarwaxa (tilapia) sosai, ki cire duk dauxar cikin kifin sai ki xauraye tas ki ajiye a gefe.

· Samo turmi sai ki vare tafarnuwa ki wanke albasa da tumatir da tattasai da attarugu da gyaxar qamshi da kanumfari sai ki jajjaga su duka ki ajiye a gefe.

· Ki xauko tukunya sai ki zuba yakuwa ki barbaxa kanwa ko ruwan toka kaxan.

· Sannan ki jera kifin a kai sai ki zuba kayan miyar da kika jajjaga a kai.

· Zuba man gyaxa da sinadarin xanxano sai ki yayyanka albasa a kai.

· Zuba rabin alayyaho a kai sai ki zuba ruwa ya cika tukuya sai ki rufe.

· Xora tukunyar a kan wuta ba mai yawa ba, sai ki bari a wuta ya dahu na kwana xaya. Kina kuma qara ruwa a-kaia-kai idan ruwan ya shanye.

· Ana bari miyar ta kwana a kan wuta domin kifin ya dahu sosai har sai qashin kifin ya yi laushi.

· Bayan kwana xaya, washe gari ke nan, sai ki buxe tukunyar ki zuba sauran alayyahon sai ki bari miyar ta nuna idan ta yi sai ki sauke. Shi ke nan miyar Marghi Special ta yi sai ci. Ba a sa cokalin miya a cikin wannan miya idan ana dafawa, sannan ba a sa wuta sosai. Ana cin wannan miya da tuwon masara, tuwon dawa, tuwon semo da tuwon shinkafa.

DUNIYAR

ha-ng

2023-05-26T07:00:00.0000000Z

2023-05-26T07:00:00.0000000Z

https://dailytrust.pressreader.com/article/281805698300896

Media Trust Limited