dailytrust

An yi riga-kafin sanqarau a Nijar bayan ya kashe mutum 100

(AFP).

Ma’aikatar Lafiya ta Jamhuriyar Nijar da haxin -gwiwar Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) sun qaddamar da shirin riga-kafin cutar sanqarau, wadda ta hallaka sama da mutum 100 daga watan Janairun bana. Cutar dai ta fi illa a yankin Zindar da ke Kudancin Nijar, inda Ma’aikatar Lafiya ta ce kawo yanzu cutar ta kashe mutum 102 daga cikin mutum 1, 810 da suka kamu da ita.

Allurar riga-kafin wadda aka faro daga 17 ga watan Mayu an ce za a kammala ta a jiya Alhamis, inda ake sa ran za a yi mutum dubu 380 allurar don ba su kariya daga cutar.

Hukumar WHO ta yi gargaxi game da bazuwar cutar daga yankin zuwa maqwabciyar qasar, wato

Najeriya lura da yadda Zinder ta yi iyaka da Jihar Jigawa.

Galibi a irin wannan lokaci akan samu vullar cutar sanqarau wadda ta saba kashe jama’a masu yawa, musamman qananan yara a shekarun da suka gabata.

Hukumar WHO ta bayyana haxarin da ke tattare da cutar, inda ta bayyana ta a matsayin mafi haxari a ko’ina a faxin qasar, kuma matsakaiciya a matakin yanki, sannan tsaka-tsakiya a matakin duniya.

Ana yawan samun varkewar cutar sanqarau a Jamhuriyar Nijar, inda a shekarar 2015 ta halaka mutum 577 a qasar, yayin da a 2017 mutum 200 suka rasa rayukansu a sanadiyar cutar.

TARE DA

ha-ng

2023-05-26T07:00:00.0000000Z

2023-05-26T07:00:00.0000000Z

https://dailytrust.pressreader.com/article/281925957385184

Media Trust Limited