dailytrust

Tambayoyi da amsoshi a kan aikin Hajji da Umara da Ziyara (3)

Daga SP Imam Ahmad Adam Kutubi

Tambaya: Mu mutanen Makka ne, mun saba kowane watan Ramadan muna yin Umara amma daga gidajenmu muke xaukar

Harama, sai kuma mu tafi Tan’im mu xauki niyya, shin hakan da muka yi ya yi ko dole sai a Tan’im za mu xaura Harami ?

Amsa: Abin da kuka yi ya yi babu laifi, matuqar cewa ba ku yi niyyar Umara ba sai a Hallu, to hakan ya halatta, insha Allah babu laifi.

Tambaya: Matata ta zo daga Gabas da daxewa ba ta yi Umara ba, sai yanzu take so ta yi, shin sai na mayar da ita inda Miqatinsu yake ta yi Harama, ko ta yi Haramarta a Makka tunda a nan muke a zaune?

Amsa: Idan lokacin da ta shigo ba ta shigo ne da niyyar yin Umara ba, saboda a nan kuke a zaune, to, idan za ta yi Umara ba sai ta koma wajen Miqatinsu na asali ba, sai kawai ta yi Harama daga Tan’im, tunda daga baya ta yi niyyar Umarar, sai kawai ta yi a Tan’im wajen da yanzu ake kira da Masallacin Nana A’isha.

Tambaya: Idan muka zo daga garinmu muka yi Umara, bayan mun huta sai muke so mu sake yin wata Umarar alhalin muna cikin Makka, shin a gidajenmu na Makka za mu yi Harama ko a Tan’im ko a wajen Miqatimmu na asali ?

Amsa: Maimaita Umara a lokaci guda bai halatta ba, sai dai ku yawaita Xawafi da Sallah da addu’a, a maimakon maimaita Umara. Mutuqar ka zo daga garinku ka yi Umara xaya ta Ramadan ta isar maka.

Amma idan ka zo ka yi Umara ba ta Ramadan ba, sai ka so ka zauna ka samu ta Ramadan, babu laifi kan hakan sai dai ba za ka yi Harama daga gidanka ba, sai ka yi Harama daga Tan’im ko Ja’aranata, ko daga Arafa, wato ka fita bayan gari ka samu tafiyar wasu ’yan mila-milai. Amma wajen da ya fi maka kusa shi ne Tan’im, ka yi Haramarka daga can ka zo ka yi Umara, wannan muna magana ne idan dama ba ka zo don yin Umarar Ramadan ba ce. A fahimta idan ta Ramadan ce ba za a sake yin wata ba, domin sahabbai ba sa maimaita Umara sai dai su yi ta Xawafi suna Sallah suna addu’o’i da karanta Alqur’ani.

Tambaya: Shin wanda ba a kewayen qasar Makka yake ba, zai zo a jirgi ya halatta ya yi Harama a cikin jirgin idan an zo saitin inda Miqati yake?

Amsa: Qwarai ya halatta idan ya zo saitin inda Miqati ya ke ya yi Harama, sai dai dole ne, sai ya yi wanka tun a garinsu idan ya zo saitin Miqatin sai ya yi niyya ya kama faxin Labbaika. Amma kamata ya yi ya tuve kayansa ya sanya Hirami da ya zo saitin wajen sai ya yi niyya, hakan ma shi ne ya fi. Domin idan ya ce sai ya zo wajen zai yi komai to kafin ya farga jirgi ya yi tafiya mai nisan da ya wuce wajen Miqatin.

Tambaya: To idan kuma mutum ya yi niyya kafin a zo wajen Miqati fa?

Amsa: Hakan ya halatta, sai dai ba’a so. Amma in ya yi niyya ce don tsoron kada a wuce bai sani ba wannan babu komai.

Tambaya: Idan mutum ya taho ta Gabas zai zo Makka don Umara a ina zai xauki Harama?

Amsa: Zai xauki Harama ce idan ya zo saitin Miqati, idan kuma a jirgi yake sai ya yi wanka a qasarsu ko a Riyad ko ma dai a ina ne abin nufi shi ne, a yi wanka a tsabtace jiki a sanya turare Sunnah ne, idan ka hau jirgi in an kusanci Miqati sai ka sanya harami, da an zo inda Miqati yake sai ka yi niyya ka fara faxin laBBAIKA… idan ma ka yi niyyar kafin a qaraso Miqati don gudun kada a wuce saboda saurin jirgi wannan babu komai. Sayyidina Umar (RA) yakan ce da waxanda ba su wuce ta wajen Miqati ba: “Ku duba ku kirdadanci inda yake a kan hanyarku.” Buhari ne ya ruwaito

Tambaya: Mun yi niyyar yin Umara daga gida inda ba qasar Saudiyya ba da muka zo filin jirgin Zaharan sai muka yi Harama, xaya daga cikinmu kuwa tun a jirgi ya yi Hamarsa, waxansu kuma sai da aka sauka a filin jirgi, amma ba mu yi raka’a biyun da ake yi in za a yi Harama ba yaya hukuncin haka?

Amsa: Babu laifi domin raka’a biyun da ake yi in za a yi Harama ba tilas ba ne, idan ka yi ta, ya fi kyau, in kuwa ba ka yi ba, ba ka da wani laifi. Haramarka ta yi, kuma da wanda ya yi Harama tun a cikin jirgi da wanda sai da aka zo filin jirgi duk Haramarsu ta yi. Muna fata Allah Ya karva.

Qwarai ya halatta idan ya zo saitin inda Miqati ya ke ya yi Harama, sai dai dole ne, sai ya yi wanka tun a garinsu idan ya zo saitin Miqatin sai ya yi niyya ya kama faxin Labbaika. Amma kamata ya yi ya tuve kayansa ya sanya Hirami da ya zo saitin wajen sai ya yi niyya, hakan ma shi ne ya fi. Domin idan ya ce sai ya zo wajen zai yi komai to kafin ya farga jirgi ya yi tafiya mai nisan da ya wuce wajen Miqatin.

Tambaya: Ni xalibi ne xan shekara ashirin da xaya, yau kwanana uku da zuwa daga Amurka, na yi yawo a jirgi daga nan zuwa can har na iso Jiddah ba ni da Harami. Da yamma na tafi Makka a gajiye da gari ya waye sai na tafi Xa’ifa don in xauki Harama a can mene ne hukuncin hakan?

Amsa: Babu laifi abin da ka aikata ka yi daidai, matuqar ka zo ne don yin Umara, to ka tafi inda Miqatinka yake shi ne abin da shari’a ta ce. Amma da a ce zuwan da ka yi ba ka zo ne don yin Umara tun asali ba, sai bayan da ka isa Makka sannan ka yi niyyar yin Umara sai ka yi Haramarka a Tan’im, Umararka ta yi muna fata Allah Ya karva.

Tambaya: Mutanen gida guda ne suka sauka a Mina amma ba su yi Harama ba, mutum biyu a cikinsu suka tafi Makka don samar musu masauki, daga baya suka dawo Mina suka je suka yi wanka suka yi Harama. Yaya hukuncin waxancan mutum biyun yake inda suka shiga Makka ba su yi Harama ba, sannan suka dawo Mina suka yi Harama a can?

Amsa: Wato ke nan sun koma wajen da ya kamata a ce daga can suka yiwo Harama, babu komai kan hakan kuma hakan ma da suka yi shi ne abin da ya fi dacewa.

SP Imam Ahmad Adam Kutubi (PhD) Zone 7 Police Headquaters Wuse Zone 3, Abuja

08036095723, 07045472372

MUSULUNCI

ha-ng

2023-05-26T07:00:00.0000000Z

2023-05-26T07:00:00.0000000Z

https://dailytrust.pressreader.com/article/281960317123552

Media Trust Limited