dailytrust

Haquri da matsayinsa a Musulunci (1)

Daga huxubar Sheikh Aliyu bn Abdurrahman Alhuzaifi, Fassarar Salihu Maqera Masallacin Annabi, Madina Huxuba ta farko

Godiya ta tabbata ga Allah wanda Ya halicci halittu kuma Ya qaddara musu abincinsu, Ya iyakance ajalolinsu ba za su mutu ba har sai sun gama cin arzikinsu da kaiwa ajalinsu. Ina gode maSa Ma’abucin tsarki, ina tuba gare Shi, ina neman gafararaSa, wanda Ya nuna hanya Ya haskaka tafarki, har zukata suka ga gaskiya suka amsa wa kiran UbangijinSu, wasu zukatan kuma suka vace, suka fifita sha’awoyinsu suka miqa musu wuya. Na shaida babu abin bautawa da gaskiya sai Allah wanda ba Ya da abokin tarayya, shaidawa ta gaskiya da yaqini, bisa imani da haqiqaninta da aiki don cim ma muradunta. Kuma na shaida Shugabanmu kuma Annabinmu Muhammad bawanSa ne kuma ManzonSa, wanda aka aiko da shiriya da addinin gaskiya, kuma da bin sa ne zukata suke kaiwa ga burinsu a Lahirarsu da duniyarsu. Tsira da Aminci da Albarkar Allah su qara tabbata a gare shi da alayensa da sahabbansa mafiya alherin al’umma, mafiya tsarki da xa’a da taqawa da sauran waxanda suka bi bayansu da kyautatawa har zuwa Ranar Sakamako.

Bayan haka, ku ji tsoron Allah Maxaukaki, ku yi maSa xa’a, domin yi maSa xa’a ne mafi tsayuwa da qarfin aiki, ku yi guzuri da taqawa domin Lahirarku. Ku sani lallai bayi suna samun fiffiko ne a wajen Ubangijinsu ta hanyar riqo da addini da kyawawan xabi’u da gaskiya, kamar yadda Allah Maxaukaki Ya ce, “Kuma ga kowane nau’i, yana da darajoji daga abin da suka aikata.” (Q: 49:19). Sannan ya zo a cikin wani Hadisin Qudusi, inda Allah Maxaukaki Yake cewa: “Yaku bayiNa! Iyaka ayyukanku ne Nake lissafo muku, sannan in ba ku lada a kansu, don haka duk wanda ya samu alheri, sai ya gode wa Allah, wanda kuma ya samu akasin haka, to kada ya zargi kowa sai kansa.”

Ya ku Muslumi! Lallai haquri xabi’a ce da siffa mai girma. Allah Ya siffanta Annabawa da Manzanni da Salihan bayi da ita, inda Yake cewa: “Saboda haka ka yi haquri kamar yadda masu qarfin niyya daga Manzanni suka yi haquri.” (Q: 49:35) da kuma faxinSa: “Kuma da Isma’ila da Idrisa da Zulkifili, dukkansu suna daga cikin masu haquri.” (Q: 21:85) da kuma faxinSa Maxaukaki: “Kuma ka yi bushara ga masu qanqantar da kai. Waxanda suke idan an ambaci Allah sai zukatansu su firgita da masu haquri a kan abin da ya same su...” (Q: 22:34-35).

Daga Anas -marfu’i- cewa Manzon

Allah (SAW) ya ce, “Imani yanki biyu ne: yanki guda haquri, xaya yankin kuma godiya.” Muslim ya ruwaito. Shi kuwa Abu Malik Al’ash’ari cewa ya yi: “Manzon Allah (SAW) ya ce, “Tsarki wani yanki ne na imani, kuma faxin alhamdu lillahi yana cika mizani, sannan faxin subhanallahi wal hamdulillahi suna cikawa-ko suna cikaabin da tsakanin sama da qasa. Sallah kuma haske ne, sadaqa kuma dalili ne, sannan haquri haske ne, kuma Alqur’ani hujja ne gare ka ko a kanka.” Ayoyi da hadisai kan haquri da falalarsa suna da yawa kuma sun shahara.

Ma’anar haquri shi ne a xaure zuciya ga aikin xa’a da kange ta daga aikata savo a kowane lokaci da sanya ta ta riqa yi wa Allah Maxaukaki xa’a a koyaushe.

Ya ku muminai! Lallai haquri yana da nau’o’i masu lizimtar juna, kuma daga mafiya girman nau’o’in haquri, akwai haquri daga barin aikata savo da abubuwan da aka haramta. Allah Maxaukaki Ya ce: “Kuma waxanda suka yi haquri domin neman yardar Ubangijinsu, kuma suka tsayar da Sallah, suka ciyar da abin da Muka azurta su da shi a asirce da bayyane, kuma suna tunkuxe mummunan aiki da mai kyau. Waxancan suna da aqibar gida mai kyau (kyakkyawar makoma).” (Q: 13:22).

Mafi yawan mutane sukan iya aikata ayyukan xa’a, su yi haquri a kan haka, amma ba za su iya haquri daga aikata savo ba, saboda haka wanda ke da qarancin haquri daga aikata haram ba zai kasance daga cikin masu haquri ba, ba zai samu darajar mujahidai masu haquri ba, domin babu mai kuvuta daga fisge-fisgen sha’awoyi, sai mai haqurin gaske, mai tsentseni na haqiqa. Duk Musulmin da ya zamo bai siffantuwa da haquri, to, wani lokaci zai zo da jin daxi na kusa ko wani xan amfani na kusa ko sha’awa mai wucewa ko wata kaba’ira mai halakarwa sai azamarsa ta gaza, iradarsa ta yi rauni, haqurinsa ya yi siriri ya dulmiya ga haram ya faxa cikin halaka, ya zama shaqiyyi babba, ya faxa a azaba mai raxaxi!

Haquri daga aikata haram kamar taya ce a jikin mota, ka suranta yadda mota za ta kasance idan babu taya, yaya makomarta zai kasance? Yaya qimarta zai zamo? Don haka idan haquri da imanin mutum ba su kange shi daga aikata haram ba, to makomarsa a duniya qasqanci ne ko kurkuku, a Lahira kuma Jahannama, tir da wannan makoma, koda kuwa mutum yana ganin ya samu rabo da girma a wannan duniya!

Nau’i na biyu na haquri shi ne: Haquri a kan yi wa Allah xa’a ta hanyar yin aikin da Ya ce a yi da yin sa daidai da yadda Ya ce a yi, da kuma haqurin dawwama a kansa. Allah Maxaukaki Ya ce: “Kuma ka bauta wa Ubanginjinka, har mutuwa ta zo maka.” (Q:15:99), sai kuma faxinSa: “Ya ku waxanda suka yi imani! Ku yi haquri kuma ku yi dauriya kuma ku yi zaman dako, kuma ku yi taqawa, tsammaninku za ku ci nasara.” (Q:3:200).

Hasanul Basri (Rahimahullah) ya ce, “An umarce su da su yi haquri a kan addininsu da Allah Ya yardar musu da shi, shi ne Musulunci. Kada su bar shi saboda yalwa ko qunci, ko tsanani ko wadata har sai sun mutu suna Musulmi. Kuma an umarce su da su daure wa abokan gaba da suke qin addininsu.”

Zaman dako shi ne dauwama a wurin ibada da tsayuwa kan umarnin Allah kada a tozarta shi.

Muslim ya ruwaito daga Hadisin Abu Huraira (RA) daga Annabi (SAW) ya ce, “Shin ba zan ba ku labari a kan abin da Allah Yake shafe laifuffuka kuma Ya xaukaka daraja da shi ba? Shi ne kyautata alwala a wuraren da ake qi (lokacin tsananin sanyi) da yawaita taku zuwa masallatai da jiran Sallah bayan Sallah, wannan shi ne zaman dakonku! Wannan shi ne zaman dakonku!! Wannan shi ne zaman dakonku!!!”

Nau’i na uku na haquri shi ne: Haquri bisa qaddara da haquri bisa masifu da abubuwan qi da suke samun bayi a wannan duniya. Wannan haquri ba ya zama abin godiya sai ya zamo tare da tsammanin lada da kuma neman yardar Allah Maxaukaki. Kuma ya zamo bawa ya san masifar abar qaddarawa ce daga Allah, kuma duk wanda ya yi haqurin za a ba shi lada, domin Allah Mai gudanar da al’amarinSa ne, wanda kuma ya riqa qara har ya fusatar da Allah, sai ya yi laifi kuma al’amarin Allah Mai gudana ne. Allah Maxaukaki Ya ce, “Kuma lallai ne muna jarraba ku da wani abu daga tsoro da yunwa da naqasa daga dukiya da rayuka da ’ya’yan itace, kuma ka yi bushara ga masu haquri. Waxanda suke idan wata masifa ta same su, sai su ce, “Lallai mu ga Allah muke, kuma zuwa gare Shi masu komawa ne. Waxannan akwai albarku a kansu daga Ubangijinsu da wata rahama, kuma waxannan su ne shiryayyu.” (Q: 2: 155 -157).

An karvo daga Anas (RA) ya ce, “Manzon Allah (SAW) ya ce, “Idan Allah Ya nufi bawanSa da alheri sai Ya gaggauto masa da uquba a duniya, idan kuma Ya nufi bawanSa da sharri sai ya qyale shi da zunubinsa har sai ya saka masa da shi Ranar Qiyama.

Ku sani girman sakamako yana tare da babban bala’i, kuma idan Allah Ya so mutane sai Ya jarrabe su da bala’i, wanda ya yarda, to, yana da yarda (daga Allah), wanda ya yi fushi, yana da (sakamakon) fushi (daga Allah)” Tirmizi ya ruwaito shi, kuma ya ce, “Hadisin ne mai kyau.”

Haqiqa Allah Ya yi umarni da haquri marar iyaka cikin faxinSa “Kuma ka yi haquri kuma haqurinka bai zama ba, face domin Allah” (Q: 16: 127), sannan Ya yi umarni da haquri a al’amura kevantattu saboda tsananin buqatar yin haquri a cikinsu, sai Ya yi umarni da haquri da hukuncin Allah shari’antacce da muqaddari, sai Ya ce, “Saboda haka ka yi haquri da huquncin Ubangijinka, kuma kada ka bi daga cikinsu mai zunubi ko mai kafirci.” (Q: 76: 24). Kuma Ya yi umarni da haquri bisa cutarwar kafirai, sai Maxaukaki Ya ce: “Lallai ne za a jarraba ku a cikin dukiyarku da rayukanku, kuma lallai ne kuna jin cutarwa mai yawa daga waxanda aka bai wa Littafi a gabaninku da kuma waxanda suka yi shirki. Kuma idan kun yi haquri kuma kuka yi taqawa, to, lallai ne wannan yana daga cikin manyan al’amura.” (Q: 3: 186).

MUSULUNCI

ha-ng

2023-05-26T07:00:00.0000000Z

2023-05-26T07:00:00.0000000Z

https://dailytrust.pressreader.com/article/281968907058144

Media Trust Limited