dailytrust

Mawaqin da aka binne da jita da tukunyar tabarsa

Kowa da kiwon da karve shi” inji musu iya magana, yayin da a wasu al’adu da koyarwar addini ake kai mutum kabari daga shi sai halinsa, a wasu al’adun kuma akan haxa masa da wasu abubuwan da ya fi so ko ya mallaka. Sarakuna da attajirai kuma a wasu wuraren da dukiya ake kai su kushewa har da gwalagwalai.

Sai dai fitaccen mawaqin nan da ya yi suna a duniya a shekarun 1970 zuwa 1980 da salon waqar Regee, Robert Nester Marley wanda aka fi sani da Bob Marley da ya rasu, da jitarsa aka kai shi kabari da kuma tunkunyar shan tabarsa, kasancewar mai son wasan qwallon kafa sai aka haxa har qwallon da yake bugawa ta nishaxi.

Tarihi ya nuna cewa mahaifin mawaqin farar fata ne, mai kula da gandun noma a qasar Jamaika. Mahaifiyarsa kuwa baqar fata ce da ta haife shi tana da shekara 19 daga karkara, ya kuma taso ne a unguwar marasa galihu (ghetto) ta Kingston a Jamaika.

Bob Marley ya kafa qungiyarsa ta kaxe-kaxe da waqe-waqe da ya sa wa suna ‘The Wailers’ ne yana saurayi sakamakon tsangwama da cin zali da kuma cin mutunci a da ya sha fama da su musamman daga ’yan makarantarsu da maqwabtansa kasancewarsa ruwa biyu da hakan ya nuna a launin fatarsa.

Wani qarin dalili na kafa qungiyar shi ne ya koka hali da yanayin zaman da suke ciki a unguwar tasu ta ya-ku-bayi a inda ya soma amfani da kixa da waqa a matsayi hanyar fita daga kangin talauci da fatara da kuma kawo sauyi a cikin al’ummarsa.

Salon kixansu ya karvu wanda hakan ya sa qungiyarsa ta ‘The Wailers’ ta yi farin jini cikin qanqanin lokaci da ta kai ga hana su wasa, saboda farin jininsu da ya shafe na manyan mawaqan waccan lokaci da aka xauke su yawon kixa. Duk da cewar qungiyarsa ta ‘The Wailers’ ta wargaje a 1974, a 1975 waqar da ya yi mai suna ‘No Woman No Cry’ ta shahara matuqa inda ta janyo masa farin jini da xaukaka a wajen qasar.

Yaqin da Bob Marley ya yi da wariya launin fata da zaluncin ’yan mulkin mallaka da kuma qoqarinsa na neman daidaito a tsakanin al’umma a waqoqinsa ya sa ya yi farin jini sosai, ya kuma zama wani gwarzo mai faxa-a-ji a tsakanin matasa.

Ya kuma samu kuxi da waxannan waqoqi sai dai an ce ya taimaka wa talakawa da marasa galihu da yawa a qasarsa ta Jamaika da dukiyar.

A 1977 aka gano ya kamu da ciwon daji a babbar yatsarsa sakamakon wata maqarqashiya ta hallaka shi da ake zargin Hukumar Leqen Asiri ta Amurka (CIA) ta yi. Mawaqin ya qi a yanke yatsar da ya kamu da ciwon. A cewarsa addininsa na Rastafariya ya haramta yin haka, sakamakon qin, ciwon dajin yayi yaxo har ya kai ga qwaqwalwarsa.

Hakan ya yi sandiyyar mutuwarsa a ranar 11 ga Mayun 1981. Shekara 42 cif-cif a wannan wata, ya rasu yana xan shekara 36 da haihuwa. Kalmarsa ta qarshe a duniya ita ce “Kuxi ba sa iya sayen rai.” An binne shi a qasarsa Jamaika a wani qasaitaccen biki na musamman.

MAKARANTA

ha-ng

2023-05-26T07:00:00.0000000Z

2023-05-26T07:00:00.0000000Z

https://dailytrust.pressreader.com/article/281998971829216

Media Trust Limited