dailytrust

Xan qasar Japan dake ya sayar da Mangwaro mafi tsada a N105,15

Wani xan qasar Japan ya shiga harkar noma da qafar dama a inda ya soma shuka

Mangwaro a matsayin gwaji, amma kuma yanayi da kasuwa suka sa Mangwaron nasa ya zama abin nema ruwa a jallo da ta sa farashinsa ya kimanin N105,15 guda kowanne xaya.

Manomin mai suna Hiroyuki Nagakawa na shuka Mangwaron nasa ne a yankin Tokachi mai dusar qanqara dake arewacin arewa na qasar, ya kuma soma shuka mangwaron ne domin sayarwa a shekarar 2011 da taimakon wani manomin ‘ya’yan itace ne mai suna Miyazaki.

Miyazaki daga kudancin qasr shi ya qarfafi Hiroyuki da ya jarraba nomana mangwaron a yanayi na hunturu wanda hakan ta sa ya kafa gonarsa a yankin mai matuqar sanyi da kuma kamfaninsa mai suna Noraworks Japan wanda a ‘yan shekaru kaxan ya soma Mangwaron da yayi masa laqabi da ‘Hakuginno taiyo’.

Ma’ana, rana a cikin a dusar qanqara.

“Da farko babu wanda ya xauka da gaske nake yi” a cewar Hiroyaki dan shekare 62 da haihuwa, wanda a da, mai gidan sayar da man fetur ne. “Daga nan Hokkaido nake so in zo da wani sabon abu ne daga albarkatun da Allah Yayi mana”.

Sanyen da farar rigar aiki a cikin xakin rainon ‘ya ‘yan itace a Otofuek da ke tsibirin Hokkaido Hiroyaki ya ci gaba da tsainkar nunannun ‘ya’yan mangwaro da za a shirya cikin mazubi da kuma kai su kasuwa.

A wajen xakin tsakiyar ne da ake yin sanyi da ya kai qasa da digiri 8 a ma’aunin Selsiyus. Amma a cikin xakin rainon yanayin zafi ne da ya nuna digiri 36 selsiyus a ma’aunin

Selsiyos.

Sirrin nasarar Hiroyiki wanda ta kai ga samar da wanan Mangwaro mai tsada shine amfani da albarkatun wurin da ya fito na asali da ake kira ‘Hokkaido’ wanda aka fi sani da tsananin hunturu da dusar qanqara, ya kuma alkinta dusar qanqarar a watannin da take zuba, sai ya sanyaya xakunan da ya ke renon itatuwan mangwaron a cikin rani.

A inda Mangwaron ke jinkirta girma da kuma nuna har sai a cikin huturu, a inda yake amfani da tafki da gulbi na ruwan zafi ya xumama xakunan renon irin. Wanda hakan ke sa mangwaron ya nuna har ta kai shi ga tsinkar aqalla Magwaro 5,000 ba a cikin yanayinsa ba.

MAKARANTA

ha-ng

2023-05-26T07:00:00.0000000Z

2023-05-26T07:00:00.0000000Z

https://dailytrust.pressreader.com/article/282007561763808

Media Trust Limited