dailytrust

Filin qwallon da jirgin qasa ke bi ana tsaka da wasa

Shin yaya za ka ji idan kana tsakiyar kallon qafa cikin filin wasa, Sai qungiyarka na daf zura qwallo a raga abokiyar karawarta hankalinku duk ya tafi kan yadda za ci qwallon sai kawai ka ji qarar jirgin qasa ya kuma zo ya wuce ta gabanka a inda kake zaune a rumfar ‘yan kallo?

Wannan ba almara ba ce, hakan abin yake a filin wasan qwallon qafa mai suna Clerny Balog na qunqiyar qwallon qafa ta TJ Tattran da ke qasar Slovakia. Inda hanyar jirgin qasa ya ratsa ta cikin filin wasan kuma daf da rumfar ‘yan kallo wanda hakan ya cigaba da xaukar hankalin mutane a duniya.

A cewar jaridar Independent ta Ingila, wucewar jirgin ana tsaka da wasan qwallo ba ya shafar wasannin da ake yi, bai kuma tava hargitsa wa ‘yan wasa ko kallo al’amarinsu na wasa ba ko kuma katsewa ‘yan kallo jin daxin wasansu ba.

A maimakon haka ma wucewar jirgin ana wasa wani abin mamaaki ne da sha’awa ga ‘yan kallo musanman farkon zuwa.

Rahotanni na cewa an gina filin wasan na Clerny Balog ne cikin shekarun 1980 a zamanin tsohuwar hukumar kula zirgazirgar jiragen qasa ta qasar. Sai dai babu wasu cikakkun bayani na dalilin da hukumar kula da raya birane ta qasaar ta yanke sha’awar gina hanyar jirgin ya kuma ratsa ta cikin filin wasan.

Kasancewar an daina amfani da irin waxannan jiragen kuma tsawon waxannan shekaru an bar hanyar jirgin tamkar wani abin ado a filin wasan ba tare an ciresu ba, ko wani abu makamancin haka.

Amma a farko shekarun 1990 wasu masu sha’awar harkar jiragen qasa suka gyara hanyar jirgin. A kuma shekarar 1992 aka buxe hanyar layin dogon domin soma amfani da shi a hukumance a matsayin wani abin kuzo-ku-gani na tarihi musamman ga ‘yan yawon buxe ido.

Tun daga lokacin kuma jiragen irin na da, masu amfani da kwal ke kai komo a layin dogon, wasu lokutan ana tsaka da wasan kwallon qafa na qungiyar.

An yi itifaqin cewa filin wasan na Cleeny Balog shine fili guda xaya tilo a duniya wanda layin dogo na jirgin qasa ya wuce ta cikinsa wanda kuma ana amfani da shi, a inda ana tsaka da wasa kuma jirgi na wucewa babu ruwnan kowa da shi duk da qarar wucewarsa da kuma ihunsa.

A lokuta da yawa na cikin jirgin ne da kuma ‘yan a kallon wasa da ke waje, ke yiwa juna adabo cikin raha da murna da kuma farin cikin wannan abin mamaki.

MAKARANTA

ha-ng

2023-05-26T07:00:00.0000000Z

2023-05-26T07:00:00.0000000Z

https://dailytrust.pressreader.com/article/282016151698400

Media Trust Limited