dailytrust

Muhimman abubuwa game da katafariyar matatar man Xangote

Daga Abbas Xalibi, Legas

Aranar Litinin da ta gabata ce Shugaban Qasa Muhammadu Buhari ya buɗe matatar fetur ta Xangote da ke Legas, qaddamarwar da ta yi armashi qwarai ta kuma xauki hankali a Najeriya da duniya baki xaya. Haka kuma taron ya samu halartar shugabannin qasashen qetare da suka haxa da shugabannin Nijar da Ghana da Togo da Senegal da wakilin Shugaban Chadi tare da gwamnanonin Najeriya da sanatoci da sauran manyan baqi.

Matatar wacce babu irinta a Nahiyar Afirka za ta tace gangar mai dubu 650.

Attajirin da ya fi kowa kuxi a Nahiyar Afirka xan asalin Jihar Kano, Alhaji Aliko Xangote ya kashe kuxi wuri na gugar wuri har Dalar Amurka miliyan 19 wajen gina matatar, wacce take da tashar samar da wutar lantarki mai qarfin migawatts 435 da kuma tashar jiragen ruwa ta kanta, sannan an samar da masana’antar yin takin zamani a cikinta.

Sai da Kamfanin Xangote ya samar da katafariyar tashar jiragen ruwa wacce ita kaxai ce ta iya xaukar manyan jiragen ruwan da suka yi ta jigilar kayayyakin da aka shigo da su domin gina matatar.

Ana sa ran matatar za ta riqa tace dukkan albarkatun man fetur ɗin da ake buqata a Najeriya da

ƙasashen masu maqwabtaka da ita.

An gina matatar ce bisa tsarin da Bankin Duniya da qasar Amurka da Turai suka shar’anta wajen gina matata. Baya ga man fetur, matatar za ta riqa tace iskar gas da dizal da man jiragen sama.

Aminiya ta kawo maku wasu muhimman abubuwa da suka kamata ku sani game da wannan katafariyar matatar man fetur kamar haka:

An gina matatar man fetur ta Xangote ne a yankin Ibeju Lekki a Jihar Legas, kuma tana da girman fili hekta 2,635.

Matata ce komai-da-ruwanka

mafi girma a duniya da za ta tace gangar mai 650,000 a kowace rana da fitar da sinadarin Polypropylene 900 KTPA.

Tana da wutar lantarki mai qarfin megawati 435, kuma tana da tankuna 177 masu xaukar lita biliyan 4.742

Matatar na iya tace kaso 100 bisa 100 na man fetur da ake buqata a Najeriya da wanda za a fitar da shi qasashen qetare.

An tsara matatar kaso 100 bisa 100 don xanyen mai na Najeriya tare da samar da sassauci don sarrafa sauran sinadaran xanyen man. Hakazalika, an tanadar mata da tashar jirgin ruwa ta musamman mafi kyan tsari a faxin duniya.

Man dizal da na fetur da matatar za ta riqa samarwa za su dace da qayyadaddun qa’idojin Turai na 9, kana tsarin matatar ya dace da qa’idojin Bankin Duniya da US EPA da qa’idojin fitarwa na Turai da ka’idojin fitar da albarkatun mai na DPR

Matatar an tsara ta ce bisa turbar fasahar zamani. Kuma an tsara ta don sarrafa ɗanyen mai iri daban-daban da suka haxar da akasarin ɗanyen mai na qasashen Afirka da xanyen mai na qasashen

Gabas ta Tsakiya da kuma man fetur na qasar Amurka.

Kamfanin Xangote yana xaya daga cikin kamfanoni qalilan a duniya da suka yi mu’amalar aikin matatar man kai-tsaye da Katafaren Kamfanin Man Fetur na duniya (EPC) matsayin xan kwangilar saye da sayarwa da kuma gine-gine.

Kamfanin Xangote ya horar da injiniyoyi matasa 900 a kan ayyukan matatar mai a qasashen waje.

Tun kafin a kai ga buxe matatar, wakilin Aminiya ya gano mazauna yankin da aka kafa matatar tuni suka fara cin gajiyar gina matatar a yankin domin baya ga raya yankin nasu da kuma tarin matasansu da ke cin moriyar matatar wajen sama masu ayyukan yi da hada-hada, Alhaji Aliko Xangote ya kuma kafa gidan burodi wanda yake samar da burodin da ake raba wa al’ummar yankin a kyauta a kowace rana. ’Yan Najeriya baki har kunne ’Yan Najeriya na murnar ganin fara aikin matatar wadda Kamfanin Mai na Qasa (NNPCL) ke da kashi 20 cikin 100 na hannun jari.

Masu ruwa-da-tsaki a vangaren mai na ganin matatar za ta sauya matsayin Najeriya daga mai shigo da tataccen mai zuwa mai fitarwa qasashen waje.

Wannan kuwa na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnatin qasar ke shirin soke biyan tallafin mai wanda kuxin da take kashewa a kai ya qaru daga Naira biliyan 351 a 2005 zuwa Naira tiriliyan 4.39 a 2022.

Duk da cewa babu tabbacin fara aikin matatar zai rage tsadar mai a qasar, amma tabbas zai rage kuxin da ake kashewa wajen jigilar man da irin asarar da ake yi.

Wasu masana na ganin za a samu sauqin farashin mai idan gwamnatin Najeriya ta ba matatar mai a farashi mai sauqi, duk da cewa kamfanin bai buqaci haka ba tukunna.

Wasu masanan na ganin fara aikin matatar zai buxe wani sabon babi a kan batun tallafin da gwamnati ke neman cirewa.

Shugaban Qungiyar Ma’aikatan Man fetur da Iskar Gas (PENGASSAN), Kwamared Festus Osifo ya ce, fara aikin matatar zai rage kuxaxen da ake kashewa wajen shigo da tataccen mai da rashin tabbacin farashinsa.

Asusun Lamuni na Duniya (IMF) ya yi hasashen cewa fara aikin matatar ta Xangote zai taimaka wajen havaka tattalin arzikin Najeriya.

Qungiyar Masu Samar da Man Fetur ta Afirka (APPO) ta ce, matatar za ta riqa samar da mai ga qasashe 12 da kuma kashi 36 na man da ake buqata a nahiyar, wanda hakan zai rage kuxin da ake kashewa wajen shigo da man zuwa nahiyar.

TUNA BAYA

ha-ng

2023-05-26T07:00:00.0000000Z

2023-05-26T07:00:00.0000000Z

https://dailytrust.pressreader.com/article/282059101371360

Media Trust Limited