dailytrust

Cristiano Ronaldo ya yi sujada bayan zura qwallo a Saudiyya

Aranar Talatar da gabata ce Kyatfin xin qasar Portugal, Cristiano Ronaldo ya yi sujada bayan ya zura qwallo a wasan qungiyarsa ta All Nassr da Al Shabbab a gasar Firimiyar Saudiyya.

Ronaldo ya zura qwallo ta uku ne bayan da Qungiyar Al Shabbab ta fara zura qwallo biyu a ragar Al Nassr.

Da a ce an doke Al Nassr a wasan, da shi ke nan sun fita a layin lashe gasar ta bana, wadda saura wasa biyu kacal a kammala.

Hakan ya sa ’yan wasan Al Nassr suka shiga tashi hankali, inda suka farke qwallo biyu, sannan aka ci gaba da fafatawa har Ronaldo ya zura qwallo ta uku.

Wannan ya sa filin wasan ya cika da murna ta vangaren magoya bayan Qungiyar

Al Nassr, inda cikin murna Cristiano Ronaldo ya faxa ya yi sujada.

Wannan nasarar ta sa har yanzu Al Nassr tana sa ran lashe gasar ta bana, inda take biye wa Al Ittihad da tazarar maki uku.

Sai dai sujadar da Cristiano ya yi ta haifar da ce-ce-ku-ce, inda wasu suke farin ciki musamman Musulmi, wasu kuma a gefe suke nuna rashin jin daxi.

WASANNI

ha-ng

2023-05-26T07:00:00.0000000Z

2023-05-26T07:00:00.0000000Z

https://dailytrust.pressreader.com/article/282067691305952

Media Trust Limited