dailytrust

Mu leqa Sudan mu ga wainar da ake toyawa (3)

YASIR RAMADAN GWALE

Da Turawa suka ga haka, sai su ma suka sauya salo, da farko ba su matsa wa al-Bashir sai ya sauka ko ya soke dokokin shari’a ba. Amma sun yi amfani da farfaganda da mutanen Sudan da suke zaune a qasashen Turai da Amurka, suka dinga kunna masa wuta iri-iri, aka dinga cinna wutar rikici da yaqe-yaqe a kusan ko’ina a qasar. Wannan ya jefa gwamnatin al-Bashir da ke da kyakkyawan quduri a cikin mawuyacin hali da faxawa halin qaqa-ni-ka-yi.

Bayan nan aka sake ingiza wutar rikicin Kudancin Sudan wanda galibin mazauna yankin ba Musulmi ba ne. Bugu da qari, aka sake kunna masa wata wutar rikici a yammacin Sudan da ya qunshi yankin Darfur da sauran sassan Sudan da dama. Baya ga haka kuma, aka sake haddasa masa yaqe-yaqe a qasashen da ke kewaye da shi, kamar Eritiriya da Habasha da Chadi da kuma rikicin qabilanci na baqaqen fatar qasar Masar da ke da iyaka da Sudan da sauransu.

Wannan ya sanya makamai da yawa suka dinga sulalewa suna shiga cikin Sudan, bayan wannan aka sanya masa takunkumin tattalin arziki iri-iri. Kusan a tsawon shekara 30 da al-Bashir ya yi a matsayin Shugaban Qasar, ya sha fama da yaqe-yaqe nan da can, ga kuma matsin tattalin arziki, a gefe guda kuma ga al’ummar qasa suna ta nuna damuwa a kan yawaitar hauhawar farashin kayan masarufi da kuma matsanancin hali da aka sake shiga sanadiyar matsin tattalin arziki.

Haka kuma mutanen da ke zaune a qasashen waje sun yi ta zuga al’ummar qasar su yi wa gwamnatin al-Bashir bore, sun yi haka ne domin amfani da halin da al’umma suke ciki, wanda cikin sauqi za su xauki duk wata zuga su bijire wa gwamnatin saboda halin quncin rayuwar, sun yi amfani da gidajen talabijin masu zaman kansu da kafafen sadarwa na Intanet, wannan ya sa Shugaba Omar Hassan al-Bashir ya shiga cikin mawuyacin hali na gaba kura baya siyaki, musamman a qarshe qarshen mulkinsa. Ya sha fama da zanga-zanga iri-iri, waxanda ta yiwu sakamakon zuga da aka dinga yi wa al’umma ne saboda matsin tattalin arziki da aka shiga.

Gani babu wani abu da ya saura, tilas ta sa Shugaba al-Bashir miqa wuya ga wasu daga cikin muradun qasashen Turai da Amurka don ya samu a sassauta wa qasarsa takunkumin tattalin arziki wanda shi ne qashin bayan jefa al’ummar qasar a cikin mawuyacin halin talauci musamman ga masu qaramin qarfi.

Wannan abin ya janyo gwamnatin al-Bashir ta yi rauni qwarai da gaske. Amma duk da haka ya yi matuqar qoqari idan aka kalli fannonin gina qasa, kusan dukkan ci gaban da Sudan ta samu na zamani da ilimi ta samu ne a qarqashin mulkin al-Bashir, duk da makirce-makirce iri-iri da ake shirya masa wajen ganin qasar ta shiga mawuyacin hali na talauci da rashin samun wadatattun kuxaxe.

A lokacin matsin ya yi wa al-Bashir yawa, ana neman yadda za a samu sassauci, daga nan ne al-Bashir ya dinga magana da Shugaban Masar na lokacin don ya shiga tsakaninsa da Amurka da Turai a rage masa yawan takunkuman da aka qaqaba wa qasar na matsin tattalin arziki. Su kuma Amurka sharaxi ne za su kafa, wato sai dai a cire kaza da kaza, a daina kaza da kaza, kuma ga dukkan alamu al-Bashir ya miqa wuya domin ya rage wasu abubuwa da yawa.

Misali a kan sassautawar al-Bashir ga Amurka ne shi ne soke Shurxah Ash-sha’abiyya, su dai waxannan wasu ’yan sanda ne kamar na Hisbah, waxanda aikinsu shi ne hana dukkan wasu ayyukan baxala da alfasha a bainar jama’a, suna hana cakuxuwar maza da mata a otal suna kuma fasa kwalaben giya a otal da wuraren tururruka. Saboda haka Amurka ta ce in dai yana so a sassauta masa takunkumin tattalin arziki dole ne ya soke waxannan ’yan Husbah da ya kafa, kuma tilas ta sa al-Bashir ya soke waxannan ’yan sanda.

Sai suka bashi sharaxi maimakon haka, ya kafa hukumar kula da jin daxi da nishaxin rayuwa wato Haikah At-Tarfeh. Bayan haka, akwai wata qungiya da Sheikh Hassan al-Turabi ya kafa ta malaman addini na duniya waxanda suke haxuwa duk shekara ana tattaunawa ana musayar ra’ayi, don haka Amurka ta ce daga cikin sharuxxan dole al-Bashir ya soke waccan qungiya da Sheikh Turabi ya kafa, kuma ya yi hakan aka soke ta.

Sheikh Hassan al-Turabi shi ne Shugaban Majalisar Qoli ta Dattawa a Sudan, kamar yadda muke cewa Majalisar Dattawa. To, a lokacin dama an samu varaka mai girma tsakanin Shugaba al-Bashir da Sheikh Hassan al-Turabi, domin su al-Turabi sun nemi cewa lokaci ya yi da Al-Bashir zai sauka daga mulki a yi sabon zave don su kawo wani Shugaban Qasa daban, a lokacin al-Turabi yana son kawo wani tsohon soja Muhammad al-Amin daga jam’iyyarsa ta masu kishin addini domin ya maye gurbin Shugaba al-Bashir.

Wannan batu ne ya sa gwamnatin al-Bashir ta sa aka kama Sheikh Hassan al-Turabi aka xaure shi, sannan qungiyarsu aka raba ta gida biyu, ta zama akwai santsi da tavo. Daga nan matsala ta kunno kai cikin gwamnati, Shugaba Al-Bashir ya kori dukkan mutanen da ke da ra’ayin al-Turabi a cikin gwamnatinsa, waxanda kuma za su barranta kansu da al-Turabi su bi gwamnati aka qyale musu muqamansu. Wannan ya janyo aka kori mutane masu kishin addini da dama daga gwamnatin al-Bashir, kuma ya bayar da dama ga ’yan dimokuraxiyya suka kunno kai cikin gwamnatinsa, haka aka dinga tafiya har zuwa shekara ta 2018.

Wannan ya sa al-Bashir ya yi saki-na-dafe, domin kuwa dukkan abubuwan da ya so ya samu bai samu biyan buqata ba, domin babu takunkumi ko xaya da aka cire masa, bayan kuma ya yi sake wasu baragurbi sun kunno kai cikin gwamnatinsa suna yi mata zagon qasa, kuma suna tare da masu tunzura jama’a. Hakan ya sa aka dinga fitowa zanga-zanga a titunan biranen Khartoum da Omdurman da Bahri tare da kira ga al-Bashir ya sauka ya kama gabansa, kuma aka yi nasara aka tumvuke shi.

Shugaban Qasar na yanzu, AbdelFatah al-Burhan shi ne jagoran sojoji da suka goyi bayan a fatattaki al-Bashir a dawo da gwamnati hannun ’yan gurguzu. Daga nan ne aka gayyato mutane daga Turai da Amurka su zo a kafa gwamnati. Al-Burhan ya kawo Abdollah Hamdook a matsayin Shugaban Qasa, wanda riqaqqen xan gurguzu ne. A lokacin maimakon su mayar da hankali a kan yadda qasar za ta fita daga halin matsi sai suka vige da sauya dokokin ilimi, inda aka wayi gari yau a ce an soke kaza a cikin manhajar karatu, gobe kuma a ce an soke lasisin gidajen rediyo masu yaxa shirye-shiryen addini.

WASANNI

ha-ng

2023-05-26T07:00:00.0000000Z

2023-05-26T07:00:00.0000000Z

https://dailytrust.pressreader.com/article/282084871175136

Media Trust Limited